Almajirai 122 da aka dawo mana da su jigawa suke dauke da Korona – Badaru

0

Gwamnan jihar Jigawa, Mohammed Badaru ya shaida wa manema labarai cewa cikin almajirai sama da 1300 da aka dawo wa jihar da su, 122 suna dauke da kwayoyin cutar Korona.

Badaru ya ce an dawo da wadannan almajirai ne daga jihohin Kano, Nasarawa, Kaduna, Gombe, Adamawa da Filato.

Ya ce tun bayan dawowa da su da aka yi Gwamnati ta killace su a sansanin da ake horas da masu Yi wa kasa hidima sannan aka yi musu gwajin dukkan su.

Sakamakon gwajin ya nuna yara 122 cikin su sun kamu da cutar.

” Sauran yaran da basu kamu da cutar ba, tuni har mun maida su ga iyayen su. Mun hada su da sabbin kayan sawa da dan kudin goro naira 10,000 ga kowani yaro.

A karshe gwamna Badaru ya ce jihar ta bude dakin yin gwajin cutar COVID-19 a da wasu cututtukan.

Share.

game da Author