NASARAWA: An kulle Majalisa bayan Coronavirus ta kashe Dan Majalisar Jiha

0

Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya bada sanarwa cewa an kufe majalisar jihar bayan daya daga cikin mambonin ta ya mutu sakamakon cutar Coronavirus.

Gwamna Sule ya ce an rufe majalisar domin a samu damar bin dukkan mambobin daya bayan daya da ma sauran duk wasu da suka yi mu’amala da mamacin a cikin kwanakin da suka gabata.

Ya ce ya zama dole a bi su domin su killace kan su kuma a yi musu gwaji.

“Kakakin Majalisa da sauran mambobi duk sun amince su killace kan su, kuma an debi sinadaran jikin su domin a auna su.

Ya ce mamacin ya yi jiyya ce a Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Keffi.

“Ya rasu ne bayan an debi sinadarin jikin sa an kai gwaji, kafin sakamako ya fito.”

Mamacin shi ne mutum na farko da ya fara kamuwa da cutar Coronavirus a Jihar Nasarawa.

Tuni ‘yan majalisa kowa ya arce, aka rufe majalisa, sannan kowa ya killace kan sa daga iyalan sa, ya na jiran sakamako daga Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC).

Gwamna ya ce za a yi duk wani kokari domin ta zakulo duk wani da ya yi mu’amala da mamacin cikin kwanakin nan, ganin cewa tsawon lokaci da dama mamacin bai taba fashin zaman majalisa ba.

Tun a ranar Alhamis aka rufe mamacin bayan an yi masa sallah a Keffi.

Share.

game da Author