Najeriya ta bayyana cewa a ranar 10 Ga Mayu za ta fara aikin kwaso ‘yan Najeriya akalla 700, wadanda dokar hana zirga-zirga tsakanin kasashe ta ritsa da su a Amurka.
Wakilin Jakadan Najeriya a Amurka da ke birnin New York, Benaoyagha Okoye ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, a madadin Ofishin Huldar Jakadancin Najeriya da ke Amurka.
Sanarwar ta ce dukkan wadanda za a kwaso din sun yi rajista ne da ofishin cewa su na so su dawo gida.
Sai dai kuma ya ce ba a rana daya za a kwaso ba. Za a bi daki-daki ne, har a kammala kwashe su baki daya
Ya ce a ranar farko za a kwaso fasinjoji 270 ne a jirgin Ethiopian Airline, wanda zai tashi daga filin jirgin Newark da ke New Jersery kai-tsaye zuwa filin jirgin sama na Abuja.
Okoye ya ce dala 1,300 ce kudin tikitin kananan yara, kwatankwacin naira N488,800. Sai kuma tikitin manya ya kama dala 1,700, daidai da naira N639,200.
Ya kara da cewa fasinjojin ne za su biya kudin da kan su. Kuma nan gaba za a fadi ranakun da za a karasa kwaso sauran, bayan an kwaso jirgin farko.
Daga nan sai ya ce amma za a nuna fifiko wajen wadanda za a fara kwasowa, ta hanyar fara kwaso wadanda suka fara yin rajista, yin la’akari da wadanda ke da shaidar zama Amurka tsawon lokacin da aka ba su bai wuce ba kafin hana jirage tashi, dattawa, masu jirajirai ko kananan yara da kuma dalibai masu dawowa gida daga kararu a Amurka.
A ranar 18 Ga Maris ne Najeriya ta hana jirage tashi da kuma sauka daga Amurka, China, Iran, Koriya ta Kudu, Jamus, Italy, Birtaniya, Switzerland, Norway, Netherlands, Japan, Australia da kuma Sweden.