CORONAVIRUS: Hanyoyi 6 da kasashe za su iya tallafa wa kananan manoma bayan dokar hana walwala

0

Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO), ta bayyana wasu hanyoyi da ta ce kasashe za su iya bi domin su agaza wa kananan manoma sakamakon dokar hana walwala (lockdown), domin kauce wa karancin zirga-zirga safarar abinci a duniya.

Wannan hukumar ta fitar da wani faifen bidiyo ne mai dauke da sakon da ta ke son isarwa a shafin ta na Twitter

https://mobile.twitter.com/FAO/status/1256135141472296960

Hukumar FAO ta ce ta lura a lokacin ‘lockdown’ kananan manoma dai ne ke fafutikar wadatar wa jama’a da abinci. Sai dai kuma su na fuskantar kalubale wajen safarar kayan abincin domin sayarwa da kuma yadda za su samu irin shukawa.

A kan haka ne FAO ta fitar wa wadannan hanyoyin hana kayan abinci yankewa a lokacin ‘lockdown

1. Ta samar da hanyar isar da kayan abincin ta hanyar dauko su daga kananan manoma.

2. Gwamnati ta rika saye daga manoman ta na tarawa yadda za ta rika raba wadanda jama’a ke bukata.

3. Ta rika hada kananan manoma da kasuwanni ba tare da sun fuskanci wani kalubalen da ka iya haddasa amfanin gonar su ya lalace ko sun tabka asara ba.

4. A zaburar da matasa marasa aikin yi wajen kwadaita musu tafarkin rungumar harkar noma.

5. A samar da tallafi ga kanana da matsakaitan masu sana’o’i.

6. A tabbatar da cewa manoma sun samu kayan inganta harkokin noman su na shekara mai zuwa.

Illar Coronavirus Ga Harkokin Noma

Hukumar FAO ta ce a halin yanzu sama da mutum milyan 820 a duniya su ke fama da karancin abinci mai iya ginawa ko rike jikin su daga hana yunwa yi wa rayuwar su barazana.

“Amma milyan 113 daga cikin su, tuni yunwa ta rarake su, ta samu gindin zama a jikin su, ta yadda ba su ma iya ciyar da kan.su, har sai sun dogara da tallafi, agaji ko wani daunin da za su tsaya jira su ci a ranar da abincin ya samu.”

Rahoton ya ce wadannan mutane sun rigaya sun kai gargara, ta yadda tilas sai an tashi tsaye an tare musu hanyar duk wata fuskantar barazanar karancin abinci da su ke fama. Saboda nan da karshen Afrilu da Mayu, hanyoyin safarar kayan abinci ka iya durkushewa.

Share.

game da Author