Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin mutum 242 da suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan ranar Litinin.
Alkaluman da NCDC ta fitar ranar Litinin, Jihar Legas ta samu karin mutum 88, 64-Kano, 49-Katsina, 13-Kaduna, 9-Ogun, 6-Gombe, 4-Adamawa
3-FCT, 1-Ondo, 1-Oyo, 1–Rivers, 1-Zamfara, 1-Borno, 1-Bauchi.
Yanzu mutum 4641 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 902 sun warke, 150 sun mutu.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Legas ta Sanar cewa adadin yawan mutanen da ke dauke da cutar Covid-19 da aka sallama a jihar sun kai 502 a jihar.
Ma’aikatar ta ce an Sallami mutum 33 da suka warke daga cutar a jihar ranar Litini.
A lissafe dai adadin yawan mutanen da aka sallama a jihar sun kai kwatan mutanen da suka kamu da cutar kuma ke kwance a asibiti a jihar.
Ma’aikatar ta ce mata 9 da maza 24 na daga cikin mutanen da aka sallama daga asibitocin kula da masu fama da cutar coronavirus dake Onikan da Eti-Osa.
Mutum 1,861 ne suka kamu da cutar a jihar.
Daga ciki 1,308 na kwance a asibiti, an sallami 502, 33 sun mutu.
Kwamishinan Jihar Lagos, Akin Abayomi, ya bayyana cewa sama da kashi 40 na wadanda ake samu dauke da cutar a jihar, ba su yarda a gano takamaimen inda suke, tserewa su ke yi, ballantana a kai su a killace su.
Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a ranar Juma’a, Abayomi ya ce wannan ne dalilin da ya sa ake ganin alkaluman wadanda suka kamu da ciwon a Jihar Legas, amma kuma ga yawan gadaje birjik a cibiyoyin killacewa, babu masu cutar da yawa.
Abayomi ya ce a yanzu ba su da lokacin farautar masu cutar a cikin gari. Abin da ke gaban su shi ne, su na gwada duk wanda suka ga ya na dauke da alamu cutar ne kawai.