Mutumin farko da ya rasu a Gombe ya jijjibo Coronavirus daga Bauchi ne

0

Gwamnatin jihar Gombe ta Sanar cewa Cutar Korona ta yi ajalin mutum na farko a jihar.

Shugaban kwamitin yaki da cutar na jihar Idris Mohammed ya bayyana haka wa manema labarai ranar Litini.

Mohammed ya ce mutumin ya rasu ranar Lahadi da karfe 4 na yamma kuma an gano baya ga cutar Korona da ya kamu da yana fama da ciwon Hawan Jini.

” Sannan an gano wannan mutum ya jijjibo cutar daga jihar Bauchi ne a makon da ya gabata. Makwabcin sa ne ya sanar da hukumar NCDC da ya lura tunda ya dawo Gombe daga Bauchi yake ta fama da matsanancin rashin lafiya.

” Ko da Jami’ar kiwon lafiya suka zo mutumin ya yi ta kokarin boye matsalar da yake fama da ita a jikinsa. Sai dai sakamakon gwajin da aka yi masa ya nuna ya dauke da kwayoyin cutar Korona.

Daga baya Allah yayi masa rasuwa.

Share.

game da Author