Najeriya za ta jaraba ruwan maganin Coronavirus na gargajiya ‘Covid-Organics’ daga Madagascar

0

Tun bayan kaddamar da wani tataccen ruwan maganin wani ganye mai kama da sabara ko barbarta, wato Ganyen Madagascar, da shugaban kasar ya ce ya na maganin cutar Coronavirus, maganin yi fara farin jini a Afrika.

Idan ba a manta ba shugaba kasar Madagascar Andry Rajoelina ya kaddamar da fara amfani da ruwan magani COVID Organics, duk kuwa da gargadin da Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi cewa babu wani maganin cutar, kuma kuskure ne a yi amfani da maganin gargajiya a ce zai iya warkar da Coronavirus.

Makonni biyu da suka wuce Cibiyar Sarrafa Magungunan Gargajiya da ke Malagasy, babban birnin Madagascar ta kaddamar da ruwan maganin Madagascar, mai suna Covid-Organics, wanda ya kunshi ganyen Artemisia, mai kama da barbarta, sabara, runhu ko taramniya, wadda kasar ke tinkaho da yalwar sa a tsibirin yankin.

“An gwada Ganyen Madagascar, ya yi aiki ga jikin wadanda aka yi gwajin a kan su, sau biyu kuma sun warke.”

Komawar daliban kasar makarantu ke da wuya, sai gwamnatin Madagascar ta tilasta cewa kowane dalibi sai an yi masa gwajin ingancin maganin Ganyen Madagascar a jikin sa, domin kariya ga cutar Coronavirus.

Shugaban kasar ya bada umarnin a raba wa dalibai da marasa galihu ruwan maganin kyauta, yayin da masu sukuni kuma aka ce da kudin aljihun su za su saya.

Manema labarai a Malagasy sun shaida ganin dandazon jerin gwanon jama’a wadanda aka sa suka bi dogon layi ana diga musu ruwan Ganyen Madagascar a jikin baki.

A Najeriya, shugaban kwamitin Shugaban Kasa kan Dakile Yaduwar cutar Coronavirus, kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya ce shugaba Buhari ya amince a karbo wannan ruwan magani daga Madagascar a gwada shi a Najeriya.

Boss Mustapha yace za a bi dukkan ka’idojin tantance magani idan aka shigo da shi kasarnan kafin a yi amfani da shi.

Tuni dai kasashe kamar su Tanzania, Comoros, Guinea-Bissau da Congo duk sun aika a kawo musu wannan magani.

A karshe ministan Lafiya, Ehinare Osagie ya bayyana cewa idan aka shigo da maganin za a duba shi kwarai sannan kuma akwai tabbacin cewa akwai irin ganyayyakin da aka hada a aka yi wannan magani a kasar nan muna shuka shi.

Share.

game da Author