Mahukuntan FCTA da gwamnati ta kafa domin tilasta mutane su kiyaye dokar hana walwala da gwamnati ta saka a Abuja ta kama matafiya 43.
Shugaban kungiyar Ikharo Attah ya Sanar da haka wa manema labarai ranar Laraba.
Idan ba a manta ba a ranar 27 ga watan Afrilu Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sassauta dokar Hana walwala a jihohin Legas da Ogun da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Attach ya ce sun kama wadannan mutane ne tun a ranar Talata a shataletalen AYA dake Asokoro.
Ya ce wasu daga cikin su sun taso daga Abuja zuwa Kaduna, Kano da Niger.
“Wata mata da muka kama da ‘ya’yan ta biyu ta shigo Abuja daga jihar Benuwai ne.
“Duk da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya saka dokar hana walwala mutane da dama na karya dokar.
Attah ya ce sun hada da direbobin da fasinjoji duka, kuma za su fuskanci hukuma.
Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin mutum 195 da suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan ranar Laraba.
Alkaluman da NCDC ta fita, Jihar Legas ta samu karin mutum 82, 30-Kano, 19-Zamfara, 18-Sokoto, 10-Borno, 9-FCT, 8-Oyo, 5-Kebbi, 5-Gombe, 4-Ogun, 3-Katsina, 1-Kaduna, 1-Adamawa.
Yanzu mutum 3145 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 534 sun warke, 103 sun mutu.