COVID-19: Mutum goma sun kamu a gidan gwamnatin Legas

0

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Legas Akin Abayomi ya sanar cewa mutum 10 dake aiki a gidan gwamnatin jihar Legas sun kamu da cutar Coronavirus.

Ya ce gwamnan jihar Babajide Sanwo-olu da uwar gidansa Joke Sanwo-olu ba su kamu da cutar ba kuma hakan shine Karo na uku da ake yi musu gwajin cutar.

Abayomi bai fadi sunayen mutum 10 da suka kamu da cutar ba amma ya tabbatar cewa su na da alaka da fadar gwamnatin jihar. ya kara da cewa wannan shine karo na farko da wasu dake da alaka da fadar gwamnatin jihar sun kamu da cutar,

Sakamakon binciken gwajin cutar da Hukumar NCDC ta gabatar ranar Laraba ya nuna cewa mutum 82 sun kara kamuwa da cutar a jihar.

Hakan ya kawo adadin yawan mutanen dake dauke da cutar zuwa 1,324 a jihar.

Daga ciki 927 na Kwance a asibiti, an sallami 358 sannan 31 sun mutu.

Abayomi ya ce gwamnati jihar na nan a kan bakanta na sassauta dokar hana walwala a jihar .

Sai dai ya yi kira ga mutanen jihar da su ci gaba da Kiyaye dokokin da gwamnati ta saka, musamman yin amfani da takunkumin fuska, yin nesa-nesa da juna da kuma wanke hannaye.

Jihar Legas ta fi yawan wadanda suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya. daga ita sai jihar Kano da Abuja.

Share.

game da Author