Gwamnonin Arewa sun daura damarar kakkabe tsarin karatu na Almajirci a yankin – El-Rufai

0

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa duka gwamnonin Arewa sun amince lallai lokaci yayi da za a kau da tsarin karatu irin na Almajirci a yankin kwata-kwata, kuma kowa na aiki tukuru don ganin haka ya tabbata.

” Mun dade muna neman yadda za a kauda da wannan tsarinn karatu na Almajirci. Almajirci bai kari su yaran da komai ba, bai kari yankin da komai ba sannan bai kari Najeriya da komai ba.

” Gara a ace an dauki yara 200 a makarantun Boko ana koyarda su yadda za su amfani kansu da al’umma, maimakon a kyale su suna watangaririya a manyan tituna suna barec-baracen abincin da zasu ci. Kowani irin salon karantarwa ne ya fi wannan tsari na Almajirici kuma za mu tabbata ya zo karshe yanzu.

” Bari ma dai kuji idan gwamnonin Arewa na yi wa wannan kokari namu rikon sakainar kashi, musu can, ni dai a Kaduna ina so in tabbatar muku cewa Almajirci ya mutu murus kenan a jihar Kaduna.

Abin da muke kokarin yi a a nan shine, bawai yaran ba za su rika zuwa makaranta bane. Da zaran an dawo makaranta, wato an bude su duk za su koma makaranta. Zamu bi gida-gida wajen iyayen su mu nuna musu cewa yin haka yanzu ya zama dole a jihar sannan mununa musa muhimmancin kula da ya’yan su a matsayin iyaye.

Tuni dai har gwamnonin jihohi dabam-dabam sun fara maida yara Almajirai jihohin su na asali. Sai dai wasu na ganin tauye musu hakki ne na iya zama da walawala a kowani jiha a fadin kasar nan.

A wannan lokaci da annobar Coronavirus ya addabi mutanen duniya, a yankin Arewa an samu yaduwar cutar ta hanyar galantoyin da almajirai suka rika yi.

A jihar Jigawa, gwamnati ta sanar ranar Alhamis cewa Almajirai 16 cikin 45 da aka yi wa gwaji sun Kamu da cutar Coronavirus daga Kano.

Wadannan Almajiran suna daga cikin daruruwan da aka dawo da su a wannan makon.

A jihar Kaduna ma , an samu almajira da dama da suka kamu da cutar. Suna killace ana basu magani.

Share.

game da Author