COVID-19: Kano 55, Jigawa 44, Bauchi 19, Yanzu mutum 3526 suka kamu a Najeriya, 107 sun rasu

0

Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin mutum 381 da suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan ranar Alhamis.

Alkaluman da NCDC ta fitar ranar Alhamis, Jihar Legas ta samu karin mutum 183, 55-Kano, 44-Jigawa, 19-Zamfara, 19-Bauchi, 11-Katsina
9-Borno, 8-Kwara, 7-Kaduna, 6-Gombe, 5-Ogun, 4-Sokoto, 3-Oyo, 3-Rivers, 2-Niger, 1-Akwa Ibom, 1-Enugu, 1-Plateau.

Yanzu mutum 3526 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 601 sun warke, 107 sun mutu.

Jihar Kano ta samu karin mutum 55 ranar Alhamis. Jihar Zamfara suma alkaluma ya nuna sun samu karin wadanda suka kamu da dama sai jihar Bauchi da Katsina.

Share.

game da Author