CORONAVIRUS: Masu boyewa ba a killace su na maida hannun agogon yaki da cutar baya – Kwararru

0

Wasu kwararru da aka tattauna da su, sun bayyana cewa dimbin wadanda ke nokewa da boyewa ba su yarda aka killace su, su na kawo gagarimar matsala da koma-baya wajen yaki da cutar Coronavirus a Najeriya.

Baya ga masu nokewa da boyewa ba a samun damar killace su, su ma masu tserewa daga wurin killacewa su na komawa cikin jama’a, su na kawo wa kokarin yaki da cutar, ta hanyar sake watsa ta cikin al’umma, kamar yadda wadanda ba su yarda a killace su ke kara watsa ta.

Rahotanni da dama sun nuna yadda masu fama da cutar Coronavirus ke arcewa daga inda aka killace su a wasu jihohi. Kamar yadda aka ga abin da ya faru a Jihar Bauchi da Barno da Kano.

Yadda masu Coronavirus ke boyewa ba a killace su

Kwamishinan Jihar Lagos, Akin Abayomi, ya bayyana cewa sama da kashi 40 na wadanda ake samu da cutar a jihar, ba su yarda a gano takamaimen inda suke, tserewa su ke yi, ballantana a kai su a killace su.

Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a ranar Juma’a, Abayomi ya ce wannan ne dalilin da ya sa ake ganin alkaluman wadanda suka kamu da ciwon a Jihar Lagos, amma kuma ga yawan gadaje birjik a cibiyoyin killacewa, babu masu cutar da yawa.

“Jami’an mu za su dauki samfurin gwajin mutum da adireshi da lambar waya. To yawancin wadanda gwaji ke nuna su na dauke da cutar, sai su tsere daga gidajen su, ba su yarda a je a dauke su a killace su.

“Wasu kuma ba adireshin gaskiya suke bayarwa ba. Sai jami’an mu au yi ta bilumbituwar neman su a cikin unguwa a rasa. Wasu kuma ka yi ta kiran lambar su su ki dauka, ko kuma idan su ka dauka, sai su rika yin kwatancen-gare, yadda ba za a iya gano inda su ke ba.”

Ba mu da lokacin farautar masu Coronavirus:

Abayomi ya ce a yanzu ba su da lokacin farautar masu cutar a cikin gari. Abin da ke gaban su shi ne, su na gwada duk wanda suka ga ya na dauke da alamu cutar ne kawai.

Ya ce a halin yanzu kuwai gadaje 569, amma 307 babu kowa a kai. Ya yi kiran jama’a cewa duk wanda aka gwada ya kamu, to killacewa ita cw mafi sauki a wurin sa. Kuma ya ce wurin garas ya ke, an inganta shi, ba kamar lokacin cutar Ebola ba.

“Manyan jami’an gwamnati na kwanciya a wurin ana killace su, ana kula da su. Ko ni na kamu da a yanzu haka, a can za a killace ni.” Inji Kwamishina Abayomi.

Dalilan da ke sa masu Coronavirus ke gudun a killace su

Rahoto ya tabbatar da cewa zuwa ranar Lahadin nan ‘yan Najeriya 4399 ne su ka kamu da cutar Coronavirus. Amma kuma abin damuwa da fargaba, shi ne yadda akasarin masu cutar sun boye, sun ki yarda a kai su a killace a Cibiyoyin Killace Masu Coronavirus.

Wani masanin harkokin Kiwon Lafiya mai suna Laz Eze, ya ce wannan abin tsoro ne matuka, domin duk wanda ya ki bari a killace shi, to zai ci gaba da yada cutar ne a cikin al’umma.

1. Fargabar yanayin yadda wurin killacewa ya ke: Masu fama da ciwon Coronavirus, wadanda bayan sakamako ya nuna su na dauke da cutar, akasari ba su kai kan su domin a killace su, saboda rashin sanin kyau da ingancin wuraren killacewar a za a kebe su. Yadda aka rika korafin rashin kyakkyawan abinci da rashin kulawa a wasu cibiyoyin, ya sa masu cutar kan ki bari a gano inda su ke, har a kai su can a killace.

2. Rashin takamaimen maganin cutar: Da yawa na ganin cewa tunda an ce babu magani, to me kuma za a killace su a yi musu? Wannan ya sa su ke ganin babu wani dalili ko ammafanin da za su bada kan su kebe su wani wuri, a bar au cikin damuwa, tsawon kwanaki da dama.

3. Rashin sanin takamaimen irin maganin da ake ba wadanda aka killace: Shi ma wannan ya kara haifar da dalilin da ya sa akasarin masu cutar su ka gwammance gara su zauna a gida. Wannan kuwa matsala ce daga bangaren gwamnati.

Rashin sanin irin magungunan sa ake sha a Cibiyar Killace Masu Coronavirus ya sa ba a gamsu da aikin da ake gudanarwa a can ba.

4. Cutar da babu magani?: Da dama na ganin cewa tunda an ce cutar ba ta da magani, to me ya sa ake cewa a killace mutum a rika kula da shi?

Dalili kenan wani babban likita mai sauna John Oghenehero ya ke shawartar gwamnati cewa sai ta kara tashi tsaye wajen kara wayar wa da jama’a kai.

5. Zargin rashin Daraja gawar mai cutar: Wasu da yawa sun gwammace su tsaya su yi jiyya a gida. Idan ma mutuwar ce, to za su mutu a cikin dangi, inda za a rufe gawar su bisa Tsarin addini ko al’adar su. Zargin NCDC na kone gawarwaki ko dagargazu da ruwan sinadarin ‘kyamical’, ya sa ake gudun killacewa, don kada majiyyaci ya mutu a hannun jami’an NCDC.

Wasu na ganin Coronavirus ‘Karya’ Ce:

Har yanzu milyoyin mutane a Najeriya na ganin cewa cutar karya ce kawai, mura da zazzabi ne kawai ke damun jama’a, amma babu wata cuta Coronavirus.

Dalili kenan likita kuma kwararren masanin magunguna, Adeolu Olusola ke ganin cewa ya kamata gwamnati ta rika nuna irin matsanancin halin da masu fama da cutar ke ciki, domin jama’a su gamsu cewa tabbas akwai cutar Coronavirus.

Share.

game da Author