Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa jinkirin biyan sojoji da sauran bangarorin jami’an tsaro ya faru ne da saboda dokar zaman gida dole, wadda ta shafi gudanar da wasu ayyukan gwamnatin tarayya.
An dai kakaba dokar zaman gida dole a jihohi da yawa na kasar nan, har da Babban Birnin Tarayya, Abuja, Abuja.
Ofishin Akanta Janar na Tarayya ya bayyana a ranar Lahadi cewa matsalar ‘lockdown’ da aka samu ya sa bangarorin hukumomin tsaron ba su samu sukunin aikawa da bayanan adadin albashin na su ba.
Kakakin Yada Labarai na Ofishin Akanta Janar, Henshaw Ogubike, ya shaida cewa amma dai a yanzu an rigaya an biya sojojin albashin na watan Afrilu tun a ranar Juma’a, 8 Ga Mayu.
Haka Ofishin Tsarin Tantance Adadin Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya (IPPIS), ya bayyana cewa an biya sojojin kudaden albashin na su tun a ranar 8 Ga Mayu.
Cece-kucen jinkirin biyan albashin ya taso ne bayan wata jarida ta buga cewa har ranar da ta buga labarin, ba a biya sojoji albashin su na Mayu ba.
Kakakin ya ce rahoton da Vanguard ta buga zai iya tunzira sojoji su bijire wa tsarin biyan albashi na gar-da-gar, wato IPPIS.
Tsarin tantance yawan ma’aikatan da ke karbar albashin gwamnatin tarayya na IPPIS, ya janyo tsaikon biyan albashi, musamman ga malaman jami’o’in kasar nan, wadanda jar yanzu su ke sa-toka-sa-katsi tsakanin su da gwamnatin tarayya.
Discussion about this post