Ya zuwa ranar Lahadi, Coronavirus ta kashe mutum 80,000 a Amurka, kamar yadda bayanan kididdiga daga rumbun tattara bayanan barnar Coronavirus mai suna worldometer.info ya nuna.
Rahoton kididdigar ya nuna cewa Coronavirus ta kashe mutum 283,876 a duniya, a cikin watanni uku.
Mutum Milyan 4,181,218 Suka Kamu A Duniya Cikin Watanni Uku:
Worldometer.info ya nuna kididdigar cewa cikin watanni uku sama da mutum milyan 4,000,000 ne suka kamu da cutar a duniya.
Ranar Lahadi aka cika kwanaki 90 da Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa “Coronavirus ta zama bala’in annoba a duniya.”
Daga ranar 11 Ga Maris da WHO ta yi wannan mummunan furuci zuwa Litinin 11 Ga Mayu, kwanaki 90 kenan. A ranar da WHO ta yi furucin, yawan mutanen da cutar Coronavirus ta kama a duniya su 118,000, wadanda ta kashe kuma kadan suka zarce mutum 4,000.
Amma zuwa yau, a Amurka kadai ta kashe sama da mutum 80,000 a Amurka kadai, yayin da mutum milyan 1, 367,638 suke fama da cutar.
Mutum 283,876 Sun Mutu A Duniya:
Yawan wadanda cutar ta kashe daga ranar da cutar ta fara kisa a duniya, yanzu sun kai mutum 283,876.
Coronavirus ta fara bayyana birnin Wuhan na China, inda a ranar 10 Ga Janairu aka fara bayyana cewa mutum 41 sun kamu da cutar.
Wadanda Ke Saurin Warkewa Daga Cutar:
Bincike ya tabbatar da cewa wadanda ba ta yi wa mummunan kamu ba, yawanci su ne ke da rabon ganin badi.
Akasari su ne wadanda su ka dan yi zazzabi da dan tari, aka ba su kulawa ta makonni biyu zuwa uku, su ka wartsake.
Wadanda Cutar Ta Fi Saurin Kashewa:
Binciken dai ya nuna ta fi kasara masu shekaru da yawa a duniya, musamman dattawa, masu cutar sanyin limomiya mai karfin da har numfarfashi ya gagare su. Sai kuma masu fama da wata cuta, su ma idan ta kwantar da su, ba ta yi musu da sauki.
Saurin Yaduwar Cutar A Yanzu:
A cikin makon da ya gabata, kididdiga ta nuna a kullum akalla mutum 80,000 sun kamu da Coronavirus a duniya. Amma kuma a baya, daga ranar 10 Ga watan Janairu har zuwa 11 Ga Maris, mutum 118,000 kadai suka kamu a duniya, 4,000 suka mutu.
Yanzu kuwa wadanda suka mutu sun haura mutum 280,000 a duniya, cikin kasashe sama da 200.
Wadanda suka kamu da cutar a Amurka, Birtaniya, Spain da Italy, sun haura yawan wadanda suka kamu a sauran kasashen duniya.
Wadanda cutar ta kashe a Italy, Faransa, Birtaniya da Spain sun kusa yawan wadanda cutar ta kashe a sauran kasashen duniya. Saboda a wadannan kasashe hudu cutar ta kashe mutum sama da 110,000
Yawan wadanda cutar ta kama a Amurka cikin mako dayan da ya gabata, sun kai yawan kashi 1 bisa 3 na wadanda suka kamu a duniya.
Idan za a iya tunawa, farkon watan Mayu din nan ne Shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana cewa illar da Coronavirus ta yi wa Amurka ta zarce illar mummunan harin Pearl Harbour da Japan ta kai wa kasar, wanda shi ne musabbanin harin makamin mukiliyan da Amurka ta kai wa Japan a Hiroshima da Nagasaki, wanda ya kawo karshen Yakin Duniya Na Biyu.