Sakataren gwamnatin tarayya, kuma shugaban Kwamitin Shugaban Kasa kan Dakile Yaduwar Coronavirus, Boss Mustapha ya yi wa ‘yan Najeriya albishir cewa su saurari sabbin matakai kan Korona daga shugaba Kasa Muhammadu Buhari ranar Litini.
Idan ba a manta ba ranar Litini ne zai cika kwanaki 14 cif da shugaban kasa ya sassauta dokar hana walwala a jihohin Legas da Ogun da babban birnin tarayya kuma ya saka dokar hana zirga-zirgar matafiya daga jiha-jiha.
Mustapaha ya ce a ranar Lahadi shi da mambobin kwamitin sa sun garzaya fadar shugaban kasa domin yi wa shugaba Buhari bayanin halin da kasa ke ciki game da dakile yaduwar annobar Korona da ayyukan da kwamitin ke ta gudanarwa zuwa yanzu.
Haka kuma Kodinatan kwamiti Sani Aliyu ya shaida wa gidan talbijin din Channels cewa shugaba Buhari zai yi wa ‘yan kasa jawabi a yau litinin.
Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin mutum 338 da suka kamu da cutar Coronavirus a kasar nan ranar Lahadi.
Alkaluman da NCDC ta fitar ranar Lahadi, Jihar Legas ta samu karin mutum 177, 64-Kano, 21-FCT, 16-Rivers, 14-Plateau, 11-Oyo, 9-Katsina
4-Jigawa, 4-Kaduna, 3-Abia, 3-Bauchi, 3-Borno, 2-Gombe, 2-Akwa Ibom, 2-Delta, 1-Ondo, 1-Kebbi, 1-Sokoto.
Yanzu mutum 5959 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 1594 sun warke, 182 sun mutu.