Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin mutum 338 da suka kamu da cutar Coronavirus a kasar nan ranar Lahadi.
Alkaluman da NCDC ta fitar ranar Lahadi, Jihar Legas ta samu karin mutum 177, 64-Kano, 21-FCT, 16-Rivers, 14-Plateau, 11-Oyo, 9-Katsina
4-Jigawa, 4-Kaduna, 3-Abia, 3-Bauchi, 3-Borno, 2-Gombe, 2-Akwa Ibom, 2-Delta, 1-Ondo, 1-Kebbi, 1-Sokoto.
Yanzu mutum 5959 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 1594 sun warke, 182 sun mutu.
A jihar Kaduna an samu jaririya ta farko ‘yar wata hudu da ta kamu da cutar Korona a jihar. Wannan jaririya ta kamu da cutar ne ta hanyar mahaifinta da ya saba balagoro daga Kaduna zuwa Kano. An dibi samfarin mahaifin jaririyar da na uwar ta domin tabbatar da haka.
Sannan kuma duka a jihar Kaduna din an samu gidan da mutum biyar ‘yan gida daya suka kamu da Korona.
Kwamishin lafiyar jihar Kaduna Amina Baloni ta bayyana haka a Kaduna.
A jihar Kano kuma , gwamna Abdullahi Ganduje ya ce gwamnati za ta tsara yadda za ta janye dokar Zaman Gida Dole da ta saka a jihar sannan kuma ya kara da cewa za a samu karin yawan wadanda za su kamu da cutar a jihar saboda karin wuraren gwajin cutar da aka kakkafa a fadin jihar.
A jihar Bauchi, kuma Shugaban Hukumar cibiyoyin Kiwon Lafiya na jihar Rilwanu Mohammed ya koka kan yadda ake samun karin yaduwar cutar Zazzabin Lassa ne a jihar. A jawabin da yayi wa manema labari a Jihar Bauchi, Rilwanu ya ce su a jihar Bauchi, Lassa ta fi tada musu da hankali fiye da cutar Korona.