A sanadiyyar barkewar rikici a kauyukan Tingno Dutse Tito, Sabon Layi da Bagashi da yake ci yaki cinyewa gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya saka dokar hana walwala na awa 24 a karamar hukumar Lamurde.
Sakataren yada labaran gwamna Fitiri, Humwashi Wonosikou, ya sanar da haka yana mai gargadin mutane da su bi wannan doka da gwamnati ta saka a karamar hukumar.
Idan ba a manta ba rikicin da ya barke a tsakanin Hausawa da ‘yan kabilar Chabo dake garin Tingno, karamar Hukumar Lamurde jihar Adamawa, ya yai sanadiyyar rayukan akalla mutum 30.
Wani mazaunin garin ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa rikin ya barke a sanadiyyar wani hatsarin mashin da aka yi ne a kauye.
Kusan duka gidajen wannan kauye an babbake su kurmus sannan da yawa daga cikin mutanen kauyukan da duk basu ma dawo ba tun da suka fantsama daji gudun tsira.
Wani mazaunin kauyen mai suna Baba ya shaida mana cewa gwamnan jihar Ahmadu Fintiri yana ficewa daga garin, sai yan Chabo suka far musu. yace zuwa safiya Asabar, sun kirga akalla mutum 40 da suke kwance a mace.
Wani shugaban al’umma a kauyen ya ce sun bizne mutum 35 ranar Asabar.
” Ba dun Allah ya sa sojoji sun iso wannan gari daga Gombe ba da yanzu kila babu kowa ma a garin.” inji wani mazaunin Tingno