Jihar Abia ta ki barin gungun wasu matasa daga Arewa su shiga jihar, bayan ta kama su boye a tsakiyar shanun da aka yi lodi cikin tirela a ranar Talata.
Wani bidiyo da aka watsa a shafin Facebook na Gwamnatin Jihar Abia, ya nuna yadda jami’ai suka sa matasan yin layi, suka ana lissafa su daya bayan daya.
Yawancin jihohin kasar nan dai sun hana zirga-zirgar motoci dauke da fasinja zuwa jihar, saboda kokakin hana yaduwa da fantaamar cutar Coronavirus.
“Jami’ai na sun shiga cikin tirelar, sai suka ga dandazon mutane a ciki sun boye karkashin shanu. Su ka ce kowa ya fito.” Haka Kwamishinan Tsaron Jihar Abia, Dan Okoli ya shaida wa PREMIUM TIMES.
Ya ce motar ta taso daga Arewa, ta keta ta Enugu, ta na kokarin shiga Abia ne aka dakatar da ita.
“Ana lekawa cikin mortar sai ga mutum 11 a tsakiyar shanu, an zakulo su, aka ce su sauko kasa.”
Okoli ya ce matasan ba su iya magana da kowane yare sai Hausa. Wannan ya sa an kasa yi musu wasu cikakkaun tambayoyin da za su iya bada gamsassun bayanai.
Okoli ya ce jami’an sa sun bar direban da shanun da ya ke dauke sun wuce.
“Saboda idan mu ka ce ba za a wuce da shanun ba, to ina tabbatar maka idan suka juya kafin su koma gida duk sun mutu.”
Ya ce ya kara samun rahoto daga jami’an na sa cewa cikin dare sun hana wasu gungun matasa wucewa, wadanda suka kama a cikin motar daukar shank, su kimanin 30.
Ya kara da cewa daga baya ne suka samu labarin cewa matasan da ke shiga su na boyewa ne karkashin shanu a cikin motocin tirela. To daga nan ne ya ce wa jami’an sa su rik shiga cikin kowace tirela mai dauke da shanu, domin zakulo duk wani dan ci-rani daga Arewa, ana fito da shi.