Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed garagadi mutane cewa bai ce a rika shan magungunan da ya rika sha lokacin da yake fama da da cutar Coronavirus ba tare da izinin likita ba. Wato maganin Chloroquine da Zithromax.
Sannan kuma gwamna Bala ya ce zai janye cewa da yayi wai Chloroquine da Zithromax, da Vitamin C ya sha, Alla ya bashi lafiya a tsawon jinyar da yayi na Coronavirus.
” An tambaye ni me na sha na warke, nace Chloroquine da Zithromax da Vitamin C likitoci suka rika bani har Allah ya bani Lafiya. Menene lai fin haka. Saboda haka ina nan akan baka ta cewa abinda na sha kenan.
“Idan mutum yana zazzabi, zai sha Chloroquine, idan cuta ce take damun sa zai sha Zithromax, idan ciwon kai ne zaka sha panadol, duk ba sai ka nemi izinin likita ba.
Idan ba a manta ba a ranar 29 ga watan Afrilu ne Mohammed ya bayyana cewa ya Sha maganin Chloroquine, Zithromax da Vitamin C’ a lokacin da ya ke kwance bashi da lafiya, har Allah ya sa ya warke daga cutar coronavirus.
Ya ce ganin ya sha ya warke ne ya umurci duk ma’aikatan kiwon lafiya dake kula da mutanen da suka kamu da cutar a jihar su yi amfani da wadannan magunguna domin warkar da mutanen dake fama da cutar.
” Na fada wa duniya lokacin da na kamu da cutar Covid-19 sannan na bayyana yadda aka yi na samu sauki.
“Likitoci sun bani maganin Chloroquine, Zithromax da Vitamin C kuma su na rika sha har na warke kuma na umurci likitoci da su yi amfani da wadannan magunguna domin warkar da mutanen dake dauke da cutar a jihar.
“A gani na Allah ne ya warkar da ni amma ya kamata mutum ya taimaki kansa da ya zauna mutuwa ta kashe shi.
“Idan ka kamu da zazzabi ka sha Chloroquine za ka warke idan ka sha Zithromax za ka warke daga cututtukan da suka kama ka.
“Likitoci ne ke bada izini a sha kowani irin magani kuma likitoci sun bani izinin in sha maganin da na sha na warke. Ni ban aiki kowa ba ya je ya sha magani ba tare da izinin likita ba.
Ya yi addu’a Allah ya warkar da duk mutanen dake fama da cutar ganin cewa har yanzu ba a samo maganin ta ba a duniya .
Mutum 83 ne suka kamu da cutar a jihar. Daga ciki 77 na kwance a asibiti an sallami shida.
Discussion about this post