Akalla kusan mutane milyan 2 ne aka tarwatsa daga gidajen su, wadanda a yanzu haka ba su da muhalli a yankin Arewa maso Gabas.
Majalisar Dinkin Duniya ce ta bayyana haka, ta bakin Jami’in Yada Labarai na Hukumar UNICEF a Najeriya, Geoffrey Njoku.
Da ya ke magana a Abuja a ranar Talata, Njoku ya ce kananan yaran da ke cikin dimbin jama’ar da ba su da muhalli, su na cikin barazanar kamuwa da Coronavirus a halin da ake ciki.
Wannan gargadin ya zo ne lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke fitar da rahoto kan makomar kananan yaran da suna rasa muhallin su, da kuma yadda za a samu hanyar magance matsalolin da suke fuskanta, na kusa da na nesa.
“Akwai mutum milyan 1.9 da suka rasa muhallin su a Arewa maso Gabas. Kashi 60 din su kuwa duk kananan yara ne yawancin su masu shekaru biyar abin da ya yi kasa.”
Rahoton ya ce a yanzu haka a duniya akwai kananan yara milyan 19 da ke zaune ba a cikin gidajen su ba, duk a sansanonin gudun hijira sakamakon tashe-tashen hankula a cikin 2019.
Rahoton ya ce dukkan wadannan kananan yara duk a cikin kasashen su suke zaman gudun hijira.
“Irin yadda cutar Coronavirus ke bi ta na ragargazar kasashen duniya, wadannan yara su na cikin barazanar yiwuwar kamuwa da cutar Coronavirus ta yi musu rubdugu.
“Dubban daruruwan yara kanana a Arewa maso Gabas a Najeriya su na zaune gefen fagen famar gumurzu da yaki. To yanzu kuma wani bala’in na neman tunkarar su, wato bala’in cutar Coronavirus.”
Rahoton ya ce ya zama tilas a gaggauta shawo kan yadda za a ceto wadannan dimbin jama’a tare da kananan yara.
Ya ce wani abin tsoro kuma shi ne irin kuncin rayuwar da za su iya fadawa bayan annobar Coronavirus, musamman karancin abinci sakamakon karyewar tattalin arzikin kasashe da dama a duniya.
Discussion about this post