An sako ‘ya’yan fitaccen malamin da aka yi garkuwa da su

0

Masu garkuwa sun saki tagwayen ‘ya’yan fitaccen malamin Musulunci, Taofiq Akewugbafold da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Taofiq din ne da kan sa ya sanar a shafin sa na Twitter cewa a taya shi murna, masu garkuwa sun sako ‘ya’yan sa da suka tsare tun a ranar da aka fara azumi.

Ya ce an sakar masa ‘ya’yan a cikin dokar jeji misalin karfe 5:30 na asubahin yau Lahadi.

Taofiq ya yi shugabancin Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Oyo, shekara takwas, tsawon zamanin gwamna Abiola Ajimobi, wanda ya sauka cikin 2019.

Ya kuma gode wa al’ummar da suka taya shi addu’a.

Cikin makon da ya wuce ne PREMIUM TIMES Hausa ta bada labarin cewa an yi garkuwa da ‘ya’yan wani fitaccen malamin Islama.

Masu garkuwa sun yi awon-gaba da ‘ya’yan wani mashahurin mai wa’azin addinin Musulunci a garin Badun, babban birnin jihar Oyo.

Masu garkuwar sun ritsa ‘ya’yan Akewugbagold da bindiga, suka karkada su a cikin mota suka arce da su.

Da ya ke bayani a shafin sa ba Facebook, inda har hotunan ‘ya’yan na sa ya saka, malamin ya ce an yi garkuwa da ‘ya’yan na sa wadanda tagwaye ne, mace da namiji a ranar Asabar da karfe 8 na dare, a lokacin bayan ya bar gida kenan ya dauki faifan tafsirin da ya ke gabatarwa.

Ya roki jama’a su taya shi addu’a Allah ya kubutar da ‘ya’yan na sa, mace da namiji, wadanda ya ce a halin yanzu mahaifiyar su ta shiga wani mawuyacin hali tun bayan tserewa da yaran da aka yi, wadanda ya ce Allah ya albarkace ta da su bayan shekara 12 da aure, sannan ta haife su.

Ya roki jama’a su taya shi roki da lallashin masu garkuwar su dubi girman Allah su saki yaran.

Kakakin Yada Labaran Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Oyo, Fadife, ya tabbatar da sace yaran. Ya ce sun samu rahoton, har ma sun yi kamun wasu da ake zargin da hannun su.

Cutar Coronavirus ba ta hana masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga da Boko Haram ci gaba da kai hare-hare ba a kasar nan.

Farkon makon da ya gabata mahara sun kashe mutum 47 a Karamar Hukumar Safana da kewaye ta jihar Katsina.

Bayan sakin yaran da masu garkuwa suka yi a yau Lahadi, PREMIUM TIMES ta tuntubi Kakakin Yada Labarai na ‘Yan Sandan Jihar Oyo, kuma ya tabbatar da an saki yaran.

Ya ce a can bays an kama wasu mutum hudu da ake zargi su na da hannu. Yanzu kuma ana kokarin kamo wadanda suka arce da yaran, kuma suka sake su daga baya.

Share.

game da Author