Akalla Jami’an Kula da Masu Cutar Coronavirus 16 ne suka kamu da cutar a Jihar Barno.
Kwamishinan Lafiya na Barno, Salisu Kwaya-Bura ne ya bayyana wa manema labarai haka a ranar Asabar, a Maiduguri.
Kwamishina Kwaya-Bura ya ce wannan ya na nuna yadda wasu irin shiga halin barazana da saida ran da Jami’an kiwon lafiyar jihar ke yi wajen sadaukar da kan su domin kokarin dakile Coronavirus a Barno baki daya.
Ya ce daga cikin jami’an kiwon lafiya 113 da suka kamu da cutar baki daya a Najeriya, 16 daga cikin su a jihar Barno ne.
Kwaya-Bura ya ce Gwamnatin Jihar Barno na ta karin daukar tsauraran matakan hana jami’an sake kamuwa da cutar.
Ya kara da cewa yanzu haka gwamnatin jihar ta bada odar kayan kariyar cuta da jami’an kiwon lafiya za su rika amfani da su, har kaya 2,000 domin rabawa ga jami’an.
Kwamishina Kwaya-Bura, wanda kuma shi ne Sakataren Kwamitin Dakile Coronavirus a Jihar Barno, ya ce zuwa yanzu dai mutum 69 ne suka kamu a fadin jihar, yayin da cutar ta kashe mutum 9 a Barno din.
Tun da farko dai Mataimakin Gwamnan Jihar Barno, Umar Kadafur, ya bai wa manema labarai hakurin fashin kwana daya da kwamitin wanda ya ke shugabanta ya yi bai yi musu bayanin komai ba.
Ya ce hakan ya faru ne saboda ayyukan da suka rincabe wa kwamitin.
Daga nan ya ce kwamitin sa na na kokarin kara yawan gadajen kwantar da masu fama da cutar, daga 100 da ake da su zuwa 500, har ma 1,000.