Shugaba Muhammadu Buhari ya saka dokar zaman-gida-dole ta kwanami 14 a Kano, biyo bayan yawan mace-macen da aka rika yi, wadanda aka rika dangantawa da musabbabin cutar Coronavirus.
Tun kafin wannan doka dama Gwamna Abdullahi Ganduje ya rigaya ya saka wata dokar ta zaman gida, amma ya bayar da wata rana daya, a ranar jajibirin fara azumi, aka fita aka yi wa kasuwannin Kano cikar da ba su taba yin irin ta a tarihin kafuwar birnin mafi yawan al’umma a Arewa ba.
Korafe-korafen Rashin Abinci: Ci gaba da zaman gida ya haifar da korafe-korafe daga bakin dimbin jama’a, akasari irin wadanda ba su da cin yau balle na gobe, har sai sun fita sun nemo. Ana ci gaba da amfani da soshiyal midiya ana watsa irin rayuwar kuncin da jama’a ke fama da ita, wanda hakan ne ya sa suke ta neman a yi musu sassauci.
Sai dai kuma a daidai lokacin da Coronavirus ta darkaki Kano da mamaya, wasu da dama na ganin cewa ganganci ne a sassauta dokar Kano, har a bayar da ranaku biyu, wato Litinin da Alhamis a fita kasuwanni a sayi kayan abinci.
Ban Goyi Bayan Sassauta Dokar Kano Ba – Sanusi Lawal
Zantawar da Sanusi Lawal ya yi da PREMIUM TIMES HAUSA ya ce lallai a wannan da jama’a ke ta mutuwa babu kakkautawa a Kano, kuskure ne babba a ce an bada ranaku hat biyu a fita kasuwa.
“Dalili na ma farko dai har yanzu babu gwaji yadda ya kamata. Allah kadai ya san yawan masu dauke da cutar.
Na biyu kuma inji Lawan, mutane da yawa ba su so a gwada su, gudun kada a killace su. To ka ga da an bude kasuwanni, kowa zai yi caaa, a cika a sake dagulewa, a gwamutsu kenan.”
Tunatarwa Ga Masu Kukan Zaman-gida – Nasiru Shehu
“Babu wanda zai ce ya na jin dadin zaman gidan nan. Ni ma talaka ne, don na kai kwana 12 ba a ci naman miya ko na naira 200 a gida na ba. To amma mene ne amfanin maigida ya fita neman abincin naira 2000 ya koma gida dauke da Coronavirus?
“Kuma bari na tuna wa masu kafa hujja da talauci su na so a bar su su fita. Wasun su wallahi ba su yarda akwai Coronavirus ba. Babu ruwan su ce dan sun kwaso cutar, ko kuma sun jangwala wa wasu cutar
“Masu cewa bakin da Allah ya tsaga ba ya hana masa abinci, idan su na tara ‘ya’ya barkatai, su ne kuma ke dawowa yanzu su na cewa yunwa za ta kashe su.”
Hankalin wasu ya fi karkara ga kudi ba Coronavirus ba:
Jama’a da dama, a cikin marasa galihun da ma masu halin a Kano, sun fi tunanin yawan ribar da za su samu a kullum idan sun fita kasuwa. Ba su damu da wata cutar Coronavirus ba. Wasu ba ganin duk abin da ya samu mutum, to daga Allah ne. Da yawa kuma ba su daukar darasi daga yawan mace-macen da ake yi a Kano. Na su tunanin bai wuce abin da Bahaushe ke cewa, “kushewar badi sai badi” ba.
Matsawar aka sassabta doka a Kano, kashi 95 bisa 100 na al’ummar jiyar ba za su kiyaye da bin ka’idojin kauce wa kamuwa ko watsa cutar Coronavirus ba. Su dai me za su fita su samu kawai.
Kano: Dambu Idan ya yi yawa, ba ya jin mai
Duk da taratsin da gwamnatin tarayya ke yi ba rabon bilyoyin kudade ga marasa galihu, sai ya yawace Kano ka na nan talakan da aka bai wa tallafin kudi ko na abinci ka rasa.
Tirelolin abinci 110 da aka ce gwamnatin tarayya ta turo a Kano, idan ka yi wa talaka wannan tambaya, zagi kawai zai antaya. Saboda bai gan su ba, kuma ya san ba samun tallafin zai yi ba. Saboda haka shi kawai a bar shi ya fita neman abinci, duk ma abin da zai faru ya faru, mai rabon ganin badi, tilas zai gani.
Tasirin Malamai wajen karyata Coronavirus:
Tabbas an samu malaman addini da dama wadanda suka rika yi wa mabiyan su fatawar karyata cutar Coronavirus. Kuma wannan abu har yau ya shiga zukatan al’ummar Arewa. A Kano ma wannan tunani ya samu gindin zama sosai.
Farkon bullar Coronavirus an rika cewa ba ta kama Musulmi. Bayan da farko an fara cewa karya ce. Da ta rika mamayar kasashen Musulmi kuma zai wasu suka rika watsa fahimtar cewa Allah ne ke fushi da mutanen da ke aikata alfasha.
Irin wadannan tunani ya ginu sosai har ta kai wasu ba ganin ko mutum dubu nawa ya shiga masallaci, cutar Coronavirus ba za ta iya shafar su ba.
Malamai da dama sun girka wa mabiyan su cewa hana bude manyan masallatai duk wata kutunguila ce ta hana Musulmi yin sallah. Babu ruwan su da tunanin cewa hatta coci-coci ma da sinagogin gine-ginen ibadar Yahudawa duk wannan doka duk ta shafe su.
Sassauta Doka: Ana wayar gari Litinin da Alhamis, masu wadannan tunani da aka yi bayani a baya, duk su ne za su gwamutsu da dimbin mutanen da za su shigo Kano daga kauyuka da garuruwa, su cika birnin da kasuwanni. Wanda ke da cutar ya watsa. Wanda ya fita gida babu cutar a jikin sa, watakila ya dauka ya tafi da wannan mummunar tsaraba a gidan sa, makwautan sa, masallacin sa da majalisar sa ya ke zaman hira.
Bahaushe ya ce, “wanda bai ji bari ba, ai ya ji hoho!”