Najeriya ta yi cinikin danyen mai na naira tiriliyan 2.3 cikin 2018 -NEITI

0

Hukumar NEITI ta fallasa cewa Gwamnatin Najeriya ta yi cinikin danyen man ferur har na naira tiriliyan 2.3 a cikin shekara ta 2018.

An buga wannan rahoton ranar Litinin a Abuja, wanda ya nuna cewa daga cikin kudaden, Hukumar NNPC ta kamfaci naira bilyan 722.3 wadanda ta ce ta biya kudin talladin mai da su, wato ‘subsidy.’

Tallafin a cewar NNPC ta shi ne kan tataccen man ferur da aka shigo da shi kasar nan cikin 2018.

Har ila yau, NEITI ta buga cewa cikin shekarar 2018 an doli danyen mai an sayar a cikin gida da waje har ganga milyan 701. Wato kenan an samu kari daga ganga milyan 688.3 da aka sayar cikin shekarar 2017.

NNPC ya lodi ganga milyan 255.6, a madadin Gwamnatin Tarayya, sai kuma manyan kamfanonin hada-hadar mai suka lodi ganga milyan 445.5 kenan.

NNPC ta yi cinikin dala bilyan 18.2 na ganga milyan 255.3 da ta loda a madadin Gwamnatin Tarayya.

Ya kamata a ce NNPC ta raba ganga milyan 160.2 a cikin gida, amma sai ta rabar da ganga milyan 107.63 a cikin 2018.

Barayi Ma Sun Kwashi Na Su Rabon

Bayanai sun nuna a cikin 2018 an saci danyen mai tare da yi wa harkar hakar mai zagon kasa har na ganga milyan 58.28.

Kenan danyen mai da aka sata cikin shekarar 2017 na ganga milyan 16.824, bai kai wanda aka sace cikin 2018 ba

A shekarar 2018 an yi asarar fetur sanadiyyar fashewar bututu har ‘cubic meters’ 204,397.07.

NEITI ta yi bayanin cewa cikin wannan shekarar za ta saki bayanin yawan danyen mai da adadin kudin da Najeriya ta samu a hada-hadar kasuwancin shekarar 2019.

Fantsamar annobar Coronavirus a duniya ya nuna cewa wannan shekara da ake ciki ta 2020, farashin danyen mai ya yi warwas a kasa.

Hakan na nuni da cewa darajar sa ta karye, don haka ba za a samu kudi da yawa ta dalilin cinikin danyen mai ba.

Share.

game da Author