Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice (Immigration) na Kasa, Mohammed Babandede, ya bayyana cewa ya gode wa Allah da ya dora masa cutar Coronavirus, saboda ta koya masa darasi a rayuwa sosai.
Babandede, wanda ya yi wannan bayani ranar Laraba da dare, kuma ya saki bidiyon a soshiyal midiya, ya kamu da cutar ce a kasar Birtaniya.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaban na shige-da-fice ya ce, “Na yi wa Allah godiya da ya dora min ciwo. Saboda wannan ciwo ya zame min sanadin shiga taitayi na tare da gane cewa ashe dai ina da dimbin masu kauna ta da yawan gaske a kasar nan.”
Babandede ya bayyana kamuwa da cutar Coronavirus tun a ranar 22 Ga Maris. Ya kilace kan sa bayan dawowar sa daga Birtaniya.
Ya ce jama’a da dama sun yi ta nuna masa so da kauna tun bayan sanarwar da ya fitar cewa ya kamu da cutar Coronavirus.
Ya gode wa daukacin Musulmai da Kiristocin da suka rika nuna jimami, alhini da damuwar halin da ya shiga.
Babandede ya gode wa daukacin ma’aikatan hukumar da sauran ‘yan Najeriya,
Ya na daya daga cikin manyan jami’an Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da suka fita kasar nan suka dawo dauke da cutar Coronavirus cikin kasar nan..
Akwai Abba Kyari, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaba Muhammadu Buhari. Sai Gwamna Nasiru El-Rufai na Kaduna, Bala Mohammed Gwamnan Bauchi da Seyi Makinde na jihar Oyo.
Babandede ya shawarci jama’a zu kiyaye sosai da ka’idojin da hukuma ke ci gaba da yadawa domin kauce wa kamuwa da Coronavirus.