AMURKA: Coronavirus ta kashe mutane sama da 2,000, sama da mutum 200,000 sun kamu da cutar

0

Amurka ta afka cikin wani mawuyacin hali baki dayan kasar, bayan da cutar Coronavirus ta kashe sama da mutum 5,000 kuma sama da mutum 200,000 suka kamu da cutar.

Kafar tattara alkaluman bayanan cutar Coronavirus mai suna Worldometers.info ce ta bayyana haka, tare da kara cewa duk da jama’a sun killace kan su a gida kuma sun daina cakuduwa, ana ganin nan da makonni kadan masu zuwa, ana tunanin akalla wadanda cutar za ta sheka barzahu za su kai 100,000 a Amurka.

Kididdigar Alhamis, wato yammacin Laraba a Amurka ta nuna sama da mutum 215,000 suka kamu da cutar, yayin da sama da mutum 5,000 ta kashe.

Amurka ce kasar da aka fi kamuwa da Coronavirus a duniya, domin ta zarce Italy, Chana, Spain, Jamus da Iran.

Sannan kuma it’s ke da kashi daya bisa hudu na yawan daukacin wadanda suka kamu da cutar a duniya.

Shi kan sa Shugaba Donald Trump ya ce, “kowa ya shirya wa fuskantar mummunan halin da za a shiga cikin makonni kadan masu zuwa.”

Coronavirus Ta Mamaye Birnin New York

Birnin New York, wanda ke daya daga cikin mashahuran birane 5 na duniya, a yanzu cutar Coronavirus ta yi masa mummunan kamu.

A ranar 1 Ga Maris, wadanda cutar ta kashe ba su kai 100 cif ba. Amma ya zuwa ranar kusan karshen Maris, mutum 965 sun mutu sanadiyyar cutar.

Daga ranar Lahadi zuwa ranar Alhamis kuma, sama da mutum 1000 sun mutu sakamakon kamuwa da cutar a birnin Ney York.

Mutane sama da 2000 a New York. Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES ta buga labarin mutuwar babban likitan tiyatar tagwayen da aka haifa kan su manne da juna, wato James Goodrich a Amurka, sanadiyyar Coronavirus.

Sama da mutane 935,000 suka kamu da wannan cuta a duniya, yayin da ta kashe sama da mutum 47,000.

Share.

game da Author