Kano ba a san ana fama da annobar cutar Coronavirus a duniya ba, daga Ashafa Murnai

0

Kano, jihar da ta fi sauran jihohin Najeriya yawan al’umma baya ga Jihar Lagos, kuma jihar da alkaluman kididdiga su ka nuna sama da murum 52,000 suka mutum a annobar 1918, wadda ta buwayi duniya, amma abin mamaki, a yanzu cikin 2020 da annobar cutar Coronavirus ta taso kasashen duniya da kisan dubban jama’a, al’umar Kano, ba su ma san da cutar ba, idan aka auna irin halin ko-in-kula da su ke yi wajen yin kaffa-kaffa daga kamuwa da cutar.

Alama daya ce za ta lura da ita ka san akwai burbushin masu kula da kan su. Ita ce idan ka shiga manyan kantina, sai ka wanke hannayen ka da ruwan sabulu tukunna.

Da ya ke ana cikin yanayin zafi ne a Arewacin Najeriya, yawancin mazauna Kano da rana ana zaune ne gungu-gungun jama’a a kasuwanni da kofar gidaje an sauraren gidajen radiyo, wadanda ke ta bayar da labaran halin da duniya ke ciki dangane da irin kisan da Coronavirus ke wa jama’a a duniya. Amma duk wannan bai sa jama’a sun shiga taitayin su. Kano ba. Babu ruwan su.

A cikin birnin Kano babu abin da aka dakatar. Hana shigowar baki daga wasu jihohi bai rage cinkoso ba, domin bakin ba su daina shigowa ba.

Motoci, babura, da motocin A Daidaita Sahu sai karakaina su ke yi. Fasinjoji kuma ga su nan a tsaitsaye gefen titi.

Gidajen abinci duk a bude, haka dukkan kasuwannin Kano. Masallatai kuwa ana ta gudanar da sallolin farilla da sallar Juma’a.

Tun karfe 4 na asubahi za ka rika jin ladanai na kiran sallah a masallatai daban-daban. Da ya ke an zo kusa da watan azumi, ana ta samun karin yawan daurin aure a Kano, yadda amarya za tayi azumi a gidan miji

ranar Asabar an daura aurarraki masu yawan gaske a a cikin Kano, kuma a masallatai daban-daban. Wakilin mu ya ga yadda Masallacin Bilal da ke bayan Asibitin AKTH, inda dandazon jama’a suka cika haraba da cikin masallacin domin daura aure da dama a masallacin.

Haka nan tarukan walimar buki da akan shirya, shi ma ba a daina ba. Haka zaman makoki ko taron Sallar jana’iza duk ba a daina cika makil ba.

A bangaren mu’amala kuwa, duk wanda ka hadu da shi, hannu zai ba ka ku gaisa. Idan ka ki bada na ka hannun, to kallon ka shigo Kano da wata bidi’a zai yi maka. Babu ruwan su day kaffa-kaffa, ballantana yin amfani da karin maganar da Bahaushe ke cewa idan gemun Dan uwan ka ya kama da wuta, to ka shafa wa naka ruwa.

Da yawan mutane da wakikin mu ya zanta da su, ya ji ra’ayin su, gani su ke yi abin kamar almara ce. Wasu gani su ke yi makarkashiya ce. Akwai masu ganin cewa, “ai Kano na cin albarkar addu’ar malamai magabata, shi ya sa Coronavirus ba ta shiga birnin ba, kuma ba za ta shiga din ba.”

“Ni ina ruwa na da wata Coronavirus? Sharri da makircin makiya Sallah ce kawai. Ya za a ce mu daina zuwa jam’i kuma mu daina musabaha ana gaisawa? Ai idan mu ka biye ta tasu, to kafin karshen wannan watan ce mana za su yi mu daina ibada kawai. Domin ga shi ma wai za a hana mu aikin Hajjin Bana.” Inji wani mai suna Husaini da ya zanta da wakilin mu a titin Zoo Road, Kano.

An tambaye shi ba ya gwnin yadda aka killace Masallatan Makka da Madina, da kuma yadda ake yawan mutuwa a wasu kasashe, sai ya ce, “ai kushewar badi sai badi.”

Masu irin ra’ayin Husaini su na da yawa, ko ma a ce su ne suka fi yawa. Ra’ayin na su na kara tasiri a zukatan jama’a, ganin cewa har yau ba a samu rahoton bullar cutar a Kano ba.

Dokar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kafa ta hana motoci shigowa ita ma ba ta da wani amfani. Domin ba ta hana shiga Kano ba. Akwai jami’an tsaro da na kiwon lafiya a kan iyakar Kaduna da Kano. Amma motocin haya suka raina. Su kuma direbobin motocin hayar, sai suka raina wa jami’an tsaron wayau su ma. Kamar yadda wakilin Premium Times ya tabbatar.

“Jami’an tsaro ba su barin a shiga da fasinjoji. Ama sai fasinja su sauka, su hau babukan acaba a tsallaka cikin Jihar Kanoda su. Daga nan sai su sake hawa motocin su su yi gaba.

Akwai kuma rahotannin da ke nuna cewa wasu fasinjojin su na yin yanke su shiga Kano ta kananan hanyoyi daban-daban.

A Kano dai babu wata dokar hana bazuwar Coronavirus da ke aiki. Domin almajiran da Gwamna Ganduje ya ce su su fita su bar garin, su na nan daram-dakam. Tun ma kafin sallar isha’i za ka rika jin muryoyin su na tashi a kofar gidaje, su na neman sadakar abinci. Da rana kuma su na gidajen jama’a su na aikace-aikacen cikin gida, musamman wanke-wanke da debo ruwa, saboda akwai unguwanni da dama a Kano wadanda ba su ma san akwai ruwan famfo a duniya ba. Kamar yadda a Kano ba a san ana annobar cutar Coronavirus a duniya ba.

Share.

game da Author