Babu wanda ya isa yayi gwajin maganin coronavirus a Afrika – Shugaban WHO

0

Shugaban Hukumar Lafiya ta duniya Tedros Ghebreyesus ya yi suka da kakkausar murya cewa babu wani masanin kimiyya ko likita da zai gwada maganin coronavirus a Afrika.

Tedros ya ce irin wannan kalamai da likitocin Faransa suka yi ya saba wa dokokin hukumar kuma ba za ta amince da shi ba.

” Bai kamata ace wai a wannan zamani da muke ciki ba za a nemi nuna bambamcin launin fata da fifiko ga wani jinsi ko yanki na duniya. Cutar ta karade duniya, ko-ina a fadin duniya sannan ace wai Afrika ne wasu ke kira da a fara yin gwajin maganin cutar fdan aka gama hada ta.”

Ya ce hukumar zata bi ka’idar yadda ake yin gwajin magunguna idan aka yi su ba tare da an zabi can ko kuma ayi a wani yanki don nuna wani bambanci ko fifiko ba.

Idan ba a manta ba wasu likitocin kasar Faransa dake aikin hada maganin coronavirus sun ce Nahiyar Afrika ce ta fi dacewa a yi gwajin maganin idan aka kammala aiki akai.

Sai dai kuma rufe bakinshi ke da wuya sai fitattun yan wasan Afrika, Samuel Eto’o da Drogba suka yi Allah Wadai da wannan kalamai na wadannan likitoci. Suka ce ba za su yadda wani ya yi gwajin maganin a Afrika ba, bayan ga ida cutar take yi musu kisan gilla har da kasar Faransa din basu za su yi gwajin a can ba.

Share.

game da Author