Gwamnatin Tarayya ta yi wa dokar kasafin kudin 2020 kwaskwarima, ta yadda za ta fasa aiwatar da duk wasu dimbin ayyukan da ta Yi alkawarin yi, amma kuma a yanzu ta ke ganin yi wa al’ummar Najeriya wadannan ayyukan ba zai yiwu ba.
Hakan kuwa ya faru ne sanadiyyar yadda annobar Coronavirus da ta barke a duniya, ta haifar da mummunan matsalar karyewar tattalin arzikin kasashe.
Babban abin da matsalar ta fi shafa ta fannin tattalin arziki, shi ne farashin danyen man fetur a duniya, wanda ya karye har zuwa kasa da dalar Amurka 20.
Danyen man fetur shi ne babbar hanyar samun kudin shigar Najeriya, wanda ta shata kintacen kudin shigar da za ta aiwatar da kasafin 2020 a bisa farashin kowace gangar danyen mai dala 57.
Karyewar darajar danyen mai a duniya, ta sa Najeriya zaman zullumi da taraddadin yadda za ta bullo wa lamarin kasafin. A karshe dai ta yanke shawarar zabtare kaso mari yawa na kasafin wanda ta ce ba za ta iya aiwatarwa ba.
Har ila yau, Gwamnatin Tarayya ta zabtare kirdadon kasafin kudi daga dala 57 na farashin kowace gangar danyen mai, zuwa dala 30 kacal. Abin da a Rurance ake kira benchmark.
Ministar Harkokin Kudade, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed ce ta bayyana cewa gwamnati ta sa gatarin yi wa kasafi sassabe, ta guntule duk wasu manyan rassan da ta san matsalar tattalin arziki da faduwar darajar danyen bai ba za su wadatar har a aiwatar da su ba.
Ta ce yanzu an shiga “mawuyacin halin da babu wani tsimi ko dabara, sai dai a fuskanci abin da zai yiwu kawai shi za a iya yi.”
A ranar 17 Ga Disamba, 2019 ne Shugaba Muhamamdu Buhari ya gabatar da kasafin naira tiriliyan 10.59. Za a kashe naira tiriliyan 4.84 wajen ayyukan gwamnati na yau da kullum da suka hada da biyan albashi, sayen kayan aiki a ofis da kuma sauran manya da kananan tsarbace-tsarbacen Gwamnatin Tarayya.
Sannan duk dai a cikin kudin za a kashe naira tiriliyan 2.46 wajen ginawa d kafa manyan ayyuka a kasar nan. Sai kuma zunzurutun naira bilyan 2.72 da za a kashe wajen biyan basussuka.
Kasafin dai tun da farko ya samu gibin naira tiriliyan 2.28, yayin da aka gindaya shi a kan cewa za a rika hako gangar danyen man fetur milyan 2.18 a kullum ana saidawa a kan dala 57.
Kasafin 2020: Baya Ta Haihu
Najeriya ta shiga halin kaka-ni-ka-yi saboda farashin gangar danyen mai ya fadi warwas har kasa da dala 20 a ranar Juma’a da ta gabata
Sai dai kuma daga baya ya dan haura sama zura dala 22 da ‘yan sulalla a sama, bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya nemi kasashen Saudiyya da Rasha su zauna su dinke barakar da ke tsakanin su, wadda masu nazarin hada-hadar danyen mai na duniya ke ganin cewa ita ce silar karyewar farashin danyen mai fiye da Coronavirus.
Yawan fetur din da kasashen ke tunkudowa ne ake ganin ya kara karyar da farashin. To idan an saisaita, kenan Najeriya ba za ta ma iya kai har ganga milyan 2.18 a kullum a kasuwa ba, sai dai ganga milyan 1.7, wadda ta yi kintacen ta da dala 30 kacal a farashin awon sikelin kasafin kudi, wato ‘benchmark’.
Zainab ta ce a yanzu abin da ya rage shi ne a zauna a tantance barcin makaho, yadda yadda za a yi dalla-dalla da kasafin, a fitar da wanda za a iya yi a shekarar 2020, a rabu da wadanda ba za a iya aiwatarwa ba, sai a wuce wurin.