Cutar Coronavirus ta kama fiye da mutum 10,000 a Afrika

0

Ofishin Hukumar Lafiya ta duniya, WHO da ke da rashe a Congo, ya ce fiye da mutum 10, 000 fadin duniya.

WHO ta yi wannan bayani a shafin ta na Twitter mai suna @WHOAFRO, cewa a can baya cutar ta fi yin kamu a manyan biranen kasashen, amma yanzu ta kara fantsama cikin sauran biranen kasashe.

Kasashen Afrika ta Kudu, Algeriya da Kamaru ne su ka fi sauran masu fama da cutar a kasashe.

Mutum 1,749 suka kamu a Afrika ta Kudu. Yayin da ta kashe mutum 13. A Aljeriya ta kama mutum @1,468 wasu 94 sun mutum.

Mutum 650 ta kama a Kamaru, wasu mutum 9 kuma suka mutu a kasar.

Sama da mutum 500 ya mutu dalilin Coronavirus a Afrika, yayin da wasu 900 suka warke daga cutar.

Cikin makon da ya gabata ne PREMIUM TIMES ta buga bayanin cewa Cutar Coronavirus ta kama fiye da mutum milyan 1 a duniya, sama da 50,000 sun mutu.

Kwanaki 100 kenan da farkon bullar cutar Coronavirus a birnin Wuhan na China, amma zuwa yammacin ranar Alhamis har ta kashe rayukan mutum 51, 558, sannan kuma sama da mutum milyan 1 (1,004,458) sun kamu da cutar.

Tantancen bayanin kididdigar alkaluma da worldometers.info ta buga ranar Alhamis da yamma, ta tabbatar da cewa daga cikin mutum sama da milyan daya da suka kamu da cutar Coronavirus a duniya, akwai wasu mutum 38,000 da ta kwantar mutu-kwakwai-rai-kwakwai. Sannan kuma an tabbatar da cewa mutum akalla 21,000 sun wartsake daga kamuwa da cutar.

Wannan ne kari na farko kusan shekaru 100 da duniya ta tsinci kan ta cikin irin wannan ko kwatankwacin irin wannan annoba.

Wani sabon bincike kuma ya nuna cewa za a iya shakar cutar ta iska.

Rayuwar al’umma a duniya baki daya ta canja, al’amurra sun tsaya cak, yayin da aka umarci bilyoyin jama’a kowa ya killace kan sa a gida.

An rufe kasuwanni, cibiyoyi, manyan masana’antu na duniya, haka zirga-zirgar jiragen sama, na kasa da na ruwa duk sun tsaya cak.

Tuni tattalin arzikin manya da kananan kasashen duniya ya karye. Farashin danyen man ferur ya yi karyewar da bai taba yi tsawon shekaru 18 ba.

Wani karin abin damuwa kuma shi ne an yi hasashen cewa cutar za ta kara cin rayuka sama da 100,000 nan gaba kafina shawo kan ta.

Irin yadda ta ke saurin fantsama shi ma abin damuwa ne. Domin a makon da ya gabata wadanda suka kamu da cutar ba su fi rabin milyan ba. Amma a cikin sati daya har wasu sama da 500,000 sun kara kamuwa da cutar a duniya.

Kididdigar alkaluman worldometers.info sun nuna a cikin wannan mako ana samu mutum 100,000 da suka kamu bayan kowane kwanaki biyu.

Kasashen Amurka, Spain da Italy ne cutar ta fi yi wa rubdugu, kasancewa ana ta yawan samun wadanda ke mutuwa tun ma ba a kai ga yi musu gwaji ba.

Sannan kuma a yanzu bayan watanni uku da bullar cutar, yawan kisan da ta ke yi a rana daya ya karu, inda a ranar Alhamis ta kashe mutum 947 a Amurka kadai.

Har yau kasashe 18 ne kadai cutar ba ta kai ga shiga ba. A Najeriya har yau wadanda suka kamu ba su kai mutum 200 ba, a daidai lokacin da ake rubuta wannan labari.

Cibiyar Masana Tattalin Arziki da ke Jami’ar Australia ta yi kiyasin cewa an yi asarar akalla dala tiriliyan 2.4 a duniya, sakamakon cutar Coronavirus.

Share.

game da Author