COVID-19: ‘Yan Najeriya 67 da suka makale a kasar Ivory Coast sun diro Legas

0

‘Akalla ‘Yan Najeriya 67 ne suka diro iyakar Najeriya dake Seme, jihar Legas bayan gwamnati ta gama tantancesu.

An garzaya da su kai tsaye zuwa wajen killace matafiya da kuma yi musu gwajin coronavirus.

Kusan duka wadanda suka dawo daga kasar ‘yan asalin jihar Osun ne kuma ko a cikin mutum 127 da suka dawo a makon da ya gabata, an samu mutum 18 da suke dauke da coronavirus.

Idan ba a manta ba gwamnatin Najeriya ta yi kira ga duk wani dan kasa da ya makale a kasashen waje kuma yana so ya dawo gida ya cika fom za a zo a dauko a dawo da shi har gida.

Yayin da kasashe da dama suka hana shiga da mutane ko dabbobi da tsuntsaye daga wata kasa zuwa wata, ita kuwa Najeriya ta shirya jajibo wasu ‘yan kasar ta daga wasu kasashe, a daidai lokacin da cutar Coronavirus ta ragargaza kasashen da suke a makale, kuma cutar a yanzu ta karkato zuwa Najeriya.

Yayin da aka shirya dawo da su, Gwamnatin Shugaba Buhari ta ce kowa shi zai biya kudin tikitin jirgin da za a maido shi Najeriya.

A kan haka ne Najeriya ta umarci ofisoshin jakadun ta da ke kasashe daban-daban su fara tattara sunayen wadanda ke da bukatar dawowa gida.

Shugabar Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana cewa gwamnari ba za ta dawo da kowa da kudin aljihun ta ba. Don haka kowa ya tanaji kudin tikiti.

Share.

game da Author