Hukumar Hana Haduwar cututtuka ta kasa ta bayyana cewa mutum 22 sun kamu da cutar coronavirus ranar Laraba.
Sakamakon gwajin da NCDC ta yi ya nuna cewa an samu karin mutum 22 daga jihohi 3 da Abuja a kasar nan.
15 a jihar Legas, 4 a Abuja, 1 a Edo, 2 a Bauchi.
Hukumar ta ce 44 sun warke sannan shida sun mutu.
Legas -145
FCT – 54
Osun – 20
Oyo – 11
Akwa Ibom – 5
Ogun – 4
Edo – 12
Kaduna – 5
Bauchi – 8
Enugu – 2
Ekiti- 2
Ribas – 1
Benuwe – 1
Ondo – 1
Kwara – 2
Delta – 1
Katsina – 1
Likitocin Kasar Chana da aka yi zawarcin su zuwa kasar nan sun Iso Najeriya.
Likitocin sun iso kasar nan tare da kayan aiki domin taimakawa gwamnatin Najeriya aiki da take yi na dakile yaduwar cutar coronavirus.
Gwamnati tayi burus da kiraye kirayen da Likitocin Najeriya da ‘yan Najeriya cewa babu wani alfanu dake tattare da gayyatar likitocin Chana su garzayo kasar nan a wannan lokaci.