CORONAVIRUS: Likitocin Chana sun iso Najeriya

0

Likitocin Kasar Chana da aka yi zawarcin su kasar nan sun Iso Najeriya.

Karamin Ministan Kiwon Lafiya, Olorunnimbe Mamora ya bayyana a taron Kwamitin Shugaban Kasa kana Coronavirus, cewa Likitocin hade da kayan aiki sun iso Najeriya domin taimakawa gwamnatin Najeriya aiki da take yi na dakile yaduwar cutar coronavirus.

Ministan Kiwon Lafiya Ehinare Osagie bai halarci taron ba, domin ya garzaya waje taran likitocin da kayan aiki.

Gwamnati tayi burus da kiraye kirayen da Likitocin Najeriya da ‘yan Najeriya cewa babu wani alfanu dake tattare da gayyatar likitocin Chana su garzayo kasar nan a wannan lokaci.

Idan ba a manta Ministan Lafiya Osagie Ehanire, ya bayyana cewa ba haka sakaka kawai Najeriya za ta bar likitoci da jami’an kiwon lafiyar da aka gayyato daga Chana su shigo kasar nan ba.

Ehanire ya ce suna sauka a filin jirgi za a yi wa kowanen su gwaji, ko da kuwa an gwada su can a baya kafin su baro Chana din.

Kungiyar Likitocin Najeriya da ma ‘yan Najeriya da dama sun yi tir da kokarin da gwamnati ke yi domin kawo likitocin daga Chana, da nufin su bayar da gudummawar shawarwarin yadda yadda yadda yadda a shawo kan Coronavirus a kasar nan.

Hukumar Kula da Cututtuka ta Kasa (NCDC), ta ce tawagar ‘yan Chana din su 18 ta kunshi likitoci, masana ki kwararru kan cututtuka, masu kula da majiyyata, kwararrun binciken magunguna da kuma manajojin kula da lafiya.

A na sa bangaren Sakataren Gwamnatin Tarayya, kuma Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa Kan Coronavirus, Boss Mustapha, ya ce a daina fargabar zuwan wannan tawaga daga Chana, domin shawarwari kadai za su bayar ga likitocin mu, ba ayyukan wasu likitoci za a kwace a ba su ba.

“Ya kamata ma a lura cewa dokar Najeriya ba ta bai wa likitocin Chana zuwa su yi aikin kula da lafiya a kassr nan ba. Don haka a daina wata fargaba ko nukura. Shawarwari kadai za su rika bayarwa, a matsayin su wadanda suka yi gwagwarmayar dakile Coronavirus.

“A wannan yanayi da mu ke ciki na tashin hankali a duniya, babu kasar da za ta ki yarda a zo a taimaka ma ta domin shawo kan wannan annoba.” Inji Sakataren Gwamnatin Tarayya.

Share.

game da Author