Buhari bai yi wa Maryam Sanda afuwa ba, ta nan a tsare – Hukumar Kurkuku

0

Hukumar Kula da Gidajen Kurkuku ta Kasa, ta bayyana cewa ba gaskiya ba ne wani labarin ji-ta-ji-tar bogi da aka yada cewa, Maryam Sanda wadda aka yanke wa hukuncin kisa na cikin wasu daurarru 70 da aka saki a Kurkukun Kuje.

An dai saki wasu daurarru 70 a matsayin kashin farko na daurarru 2,700 da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa afuwa, domin a rage cinkoso a gidajen kurkuku, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta nemi shugabannin kowace kasa su yi, domin a guje wa yaduwar cutar Coronavirus a gidajen kurkuku a duniya.

Kakakin yada labarai na kurkuku, Mista Njoku, ya ce, “BA gaskiya ba ne labarin da ake watsawa wai an yi wa Maryam Sanda afuwa. Har yanzu ta na tsare, domin ba ta cikin rukunin wadanda aka yi sa afuwa.

“Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ya bayyana rukunin daurarru da afuwar ta shafa, da suka hada da tsoffin da suka haura shekaru 60 a duniya, kuma wa’adin su ya kusa, da sauran su. Sannan wadanda ba su a tsarin afuwar har da wadanda aka suka yi kisa.”

An dai samu Maryam Sanda da laifin kashe mijin ta, Bilyaminu Haliru, a Abuja.

Duk da dai ta daukaka kara, amma ba a fara zaman sauraren karar ba, Njoku ya ce Maryam har yanzu ta na tsare, domin na ta cancanci shiga cikin rukunin wadanda ya kamata a yi wa afuwar ba.

A na sa bangaren Shugaban Hukumar Kula da Gidajen Kurkuku na Kasa, ya ce a yi watsi da duk wani labarin da ya shafi batun afuwar Maryam Sanda domin a yanzu dai kam BA gaskiya ba ne, har yanzu ta na nan a tsare.

Share.

game da Author