Ni da kaina zan fadi ko na warke daga COVID-19, ba ‘yan kadifiri su rika aran bakina suna ci min albasa ba – El-Rufai

0

Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana cewa a daina yi masa riga malam masallaci a maganan rashin lafiyar da yake fama da shi, wato ciwon COVID-19 da yake fama da.

El-Rufai ya ce har yanzu yana nan dauke da cutar ba a wanke shi ba tukunna, kuma ma idan aka sallameshi da kansa zai fito ya fada wa mutane, ba a rika yi masa zumudin fadi ba.

Gwamna Nasir El-Rufai ya ya jagoranci taron majalisar zartaswar jihar da aka yi ta yanar gizo da manyan jami’an gwamnati.

Gwamna Nasir, da kansa ya rubuta a shafinsa ta tiwita, sannan ya kara da cewa kada mutane su rika biye wa labaran karya koda suna so sun jin abinda aka ruwaito.

Idan ba a manta ba gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da kan sa ya fadi wa mutane cewa ya kamu da cutar COVID-19 a ranar 28 ga watan Maris.

Yanzu yayi kwanaki 20 cur kenan yana killace tun bayan sanar da cewa ya kamu da cutar.

Share.

game da Author