CORONAVIRUS: Makonni 4 bayan kwantar da dan Atiku Abubakar, har yau bai rabu da cutar ba

0

Makonni hudu kenan tun bayan samun Mohammed Atiku Abubakar da cutar Coronavirus, amma har yau ba ta rabu da jikin sa ba.

Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa duk da babu wani alamun cutar a jikin sa, amma duk lokacin da aka auna shi, sai gwajin ya nuna cewa har yanzu akwai cutar a jikin sa, wato ‘positive’ kenan.

Majiyar da ta nemi a sakaya sunan ta, saboda ba a yarda ta yi magana a madadin majiyyaci ba, ta ce Mohammed na samun kaykyawar kulawa, ya shan ingantattun magungunan inganta makaran kariyar garkuwar jikin sosai, wato ‘immune boosters, amma duk da haka idan an.gwada shi, sai jikin sa ya nuna har yanzu ya na dauke da ita.

Wadanda PRWMIUM TIMES ta zanta da su, sun ce ba su taba ganin mai irin wuyar sha’anin kamuwa ko warkewa da cutar ba, kamar Mohammed Atiku.

Mohammed wanda tun bayan da aka sanar ya na da ita, ya ke a killace a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada, inda ake kwantar da masu cutar a Abuja, ya shafe kwanaki 28 kenan ya na killace.

Wasu da aka samu da cutar irin su Gwamna Bala Mohammed na Bauchi da Seyi Makinde, Gwamnan Oyo, tuni har sun warke, sun ci gaba da harkokin su.

Da ta ke wa PREMIUM TIMES karin bayani, Dakta Ifeoma Ezeonu ta Asibitin Koyarwa na Jami’ar Enugu, wadda masaniyar kwayoyin halitta da kwayoyin cututtuka ce, ta ce babu takamaimen adadin lokacin da za a ce mai dauke da cutar Coronavirus ya dade kafin ya warke. Amma dai ba ya wuce kwanaki 37.

Ta ce mai wuyar sha’anin warkewar cuta kamar Mohammed Atiku, za a xi gaba da killace shi ne, ana ba shi magungunan bunkasa makaran jikin sa har ya warke.

Mohammed na killace tun a ranar 19 Ga Maris, 2020.

Share.

game da Author