Shugaban hukumar Lafiya ta duniya Tedros Ghebreyesus ta bayyana cewa barazanar shugaban kasar Amurka Donald Trump bai dada hukumar da kasa ba cewa ita yadda za a akawo karshe cutar coronavirus shine ya fi damunta sannan tafi maida hankali a kai.
Idan ba a manta ba Trump ya yi barazanar dakatar da tallafin da kasar Amurka ke baiwa hukumar Lafiyar daga yanzu.
Sai dai kuma hukumar tace hakan bai dada ta kasa ba domin za ta ci gaba da aiki tukuru wajen ganin an samu nasara a yaki da kauda annobar coronavirus da ake yi a duniya.
Tedros ya kara da cewa hukumar tana jinjina wa kasar Amurka bisa gudunmawar da take ba hukumar, wadda ita ce tafi kowacce kasa bada tallafi ga hukumar.
” Barazana ba zai hana mu yin abinda ya kamata ba a hukumar WHO. Zamu ci gaba da tattaunawa da kasashen da muke aiki da su domin ganin ba a samu cikas ba wajen wadata hukumar da kudaden da zata bukata na aiki.
Sannan kuma Tedros ya tunatar da kasashen duniya cewa wannan hukuma ba ta wani bane ko kuma ta wata kasa musamman. An kafa ta ne domin taimakawa kasashen duniya da basu da karfin kiwon lafiya da kuma fada da cututtuka da suka addabi kasashen su
” Ba a kafa WHO don nuna fifiko ba ko kuma wani kasa ya rika nuna karfin iko, ko kuma banbacin launin fata da wariya. Don haka, hukumar zata ci gaba da aiki akan dokokin da aka kafata ne ba tare da ta kauce ba don dadada ma wata kasa ko wani rai ba.