COVID-19: Rashin iya gano wadanda suka kamu da cutar na ci mana tuwo a kwarya a Najeriya- NCDC

0

Shugaban hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa, NCDC Chikwe Ihekweazu ya bayyana cewa rashin gano mutanen dake dauke da alamun cutar coronavirus da rashin kiyaye sharuddan dauka jini domin a aika wuraren yin gwajin cutar na daga cikin matsalolin dake ci wa hukumar tuwo a kwarya wajen yake da cutar.

Ihekweazu ya fadi haka ne ranar Talata a Abuja a zaman da kwamitin shugaban kasa kan hana yadawar coronavirus ta yi.

Ya ce hukumar bata da matsalar wuraren gwajin cutar da ake da su a kasar nan.

“Yanzu za mu yi amfani da hutun makonni biyu da gwamnati ta kara wajen ganin mun inganta aiyukan gano mutanen da suke nuna alamun cutar, ta hanyar da ya kamata domin aikawa wuraren yin gwajin ba tare da jinin ya gurbata ba.

Ihekweazu ya ce gwamnati ta gina wuraren yin gwajin cutar guda 12 a kasar nan da ke yi wa mutum 1,500 gwaji a duk rana.

Ya kuma ce Hukumar na kokarin ganin an kara yawan wuraren yin gwajin cutar da ake da su a jihohin kasar nan.

Idan ba a manta ba a ranar Litini Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kara kara wa’adin kwanakin zaman gida dole a Abuja, Legas da Ogun da Kwanaki 14.

Buhari ya ce ya yi haka ne domin a samu nasaran dakile yaduwar cutar a kasan.

Sannan a ranar Talata ne Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar cewa mutane 362 ne ke dauke da cutar a Najeriya.

Cutar ta bullo a jihohi 19 a kasar nan.

99 sun warke sannan 11 sun mutu.

Share.

game da Author