Ministan babban birnin tarayya Abuja Musa Bello, ya bayyana cewa an sallami mutum 9 da aka tabbatar sun warke daga cutar coronavirus a Abuja.
Ya Sanar da haka ne ranar Laraba a shafinsa na tiwita.
Yanzu adadin yawan mutanen da aka sallama daga Abuja sun kai 20.
Bello ya ce an sallami mutum bakwai daga asibitin Gwagwalada sannan biyu daga asibitin Abuja.
Ya yi kira ga mutane da su ci gaba da kiyaye dokar hana walwala da gwamnati ta saka sannan a rika wanke hannaye da ruwa da sabulu tare da nisanta kai daga taron mutane domin samun kariya daga kamuwa da cutar.
Haka kuma an sallami mutum uku a jihar AkwaIbom.
Kwamishinan Lafiya na jihar Emmanuel Ekwuem ya bayyana ce cewa mutanen na daga cikin mutum byar da suka kamu da cutar a jihar.
Ya ce sai da aka gwada su sau biyu aka tabbatar sun warke kafin aka sallame su.
Bayan haka, an samu karin wani da ya kamu a jihar ranar Talata.
Idan ba a ranar Talata ne hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta Sanar cewa mutane 362 ne ke dauke da coronavirus a Najeriya.
An gano haka ne daga jihohin 19 a kasan.
An sallami 99 sannan 11 sun mutu.
Discussion about this post