CORONAVIRUS: ‘Yan Najeriya suna yi wa doka taurin Kai, za a saka sabbin tsauraran matakai – Gwamnati

0

Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ya koka kan yadda ‘yan Najeriya suke Yi was dokar gwnati kunnen uwar shegu game da cutar coronavirus.

Lai Mohammed ya ce a dalilin haka gwamnati za ta saka sabbin tsauraran matakai da tilasta mutane bin doka da karfin tsiya.

Lai ya ce ana yin haka ne domin kara mutane daga fadawa cikin halin kakanikayi hada da ita kanta gwamnati.

Matakan da za a saka sun hada da

1 – Za a dakatar da tafiye-tafiye zuwa jihohi da gari-gari

2 – Za a rufe duka tashoshin mota kake fadin kasar nan da na jirgin kasa kaf.

3 – Za ayi wa garuruwa da birane feshi.

Bayan haka, Lai Mohammed ya Kara da cewa gwamnati na samun matsala wajen gano wadanda suka shigo kasa Najeriya daga kasashen waje yanzu saboda da yawa daga cikin su sun bada adireshin karya ne.

” Idan muka je duba su, sai aga Ashe adireshin karya ne suka rubuta.

A karshe ya karyata rade-radin da ake ta yadawa wai na’urar shakar numfashi guda daya ne tal ake da shi a Abuja kuma wai an Kai wa fadar shugaban Kasa da ita Buhari ke shakar numfashi.

Ya ce hakan ba gaskiya bane. Sannan kuma ya koka kan yadda wasu kafafen yada labarai, ke yada labaran karerayi, labaran da basu tantance gaskiyar ta ba.

Share.

game da Author