FARGABAR CORONAVIRUS: Zaharadden Sani ya killace kansa na kwana biyu

0

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa Kannywood ya bayyana wa wakilin PREMIUM TIMES a Kaduna cewa fargaban gwajin jinin Ali Nuhu da aka ce za ayi kan cutar coronavirus ya dimauta shi har ya killace kansa nan da nan.

Zaharaddeen ya ce har ya dan yi wasiyyoyi ga iyalan sa cewa to ta-fa faru ta Kare, domin kila ya kamu da cutar coronavirus.

Babban dalilin fadin haka kuwa shine ya na daga cikin wadanda suka yi cudanya da Ali Nuhu a wadannan kwanaki.

” Ali Nuhu jarumi ne a sabon fim dina da na gama dauka mai suna Haduwar Hanya.

” Mun tafka mu’amula da cudanya matuka tare, kaga ko idan kaji irin haka dole hankalin ka ya tashi.

Zaharaddeen ya ce yana jin haka sai ya koma gida ya killace kan sa ya dan yi wasiyyoyi, sannan ya yi sallama da karen sa, jarumin fim din Haduwar Hanya sai ya killace kance.

” Matata tana ta kuka, Ina gefe tana gefe can muka yi sallama. Tun a lokacin na fara jin tashin hankali dan rabuwar da zamu yi idan har na kamu zuwa Allah ya bani lafiya.

Jarumin ya ce hankalin shi bai kwanta ba sai da suka yi waya da jarumi Ali Nuhu ya shaida masa cewa, an wanke su, sannan an ce su ci gaba da harkokin su, basu dauke da cutar.

Zaharaddeen ya gode wa Allah sannan ya yi kira ga yan uwansa da mutanen Arewa da Najeriya baki daya da su bi umarnin gwamnati, a rika tsaftace jiki sannan a rika zama wuri daya har zuwa a iya shawo kan wannan cuta.

Shima jarumi Ali Nuhu ya yi irin wannan Kira ga mutane da su mai da hankali wajen tsaftace muhalli da jiki, da kuma tsayawa wiri daya banda yawo.

Share.

game da Author