Jan-kafa da tafiyar-hawainiyar da ake yi wajen daukar kwararan matakai ke sa jama’a ba su daukar gargadin kiyayewa da hukuma ke yi musu da muhimmanci.
Har yanzu ‘yan Najeriya ba su yi amanna da mummunar illar da Coronavirus ke
haifarwa a duniya ba, duk kuwa da cewa kasa da mutum 60 har sun kamu a kasar nan.
Idan ba a gaggauta daukar mataki ba, to gaba dayan mu kowa na iya kamuwa. Wannan mahuyacin halin da ake ciki, a daidai lokacin da farashin danyen man fetur ya fadi kasa warwas, zai iya durkusar da tattalin arzikin kasar nan dungurugum. Shi ya sa mu ke kira ga hamshakan biloniyoyin kasar nan da su tashi tsaye su kawo dauki.
Shugabannin kasashen Afrika da jiga-jigan ta duk suna ta daka tsalle da murnan gudunmawar kayan gwaji da rigunan sakawa safar hannu da fuska har sama da miliyan daya da Jack Ma ya aiko wa kasashen Nahiyar da su, mai maimakon su yi koyi da haka ne su bude aljihun su su yi irin wannan jarumta wadda shine talakawan kasar nan ke nema a wannan lokaci.
Haka gidauniyar Bill da Melinda Gates duk sun bada irin wadannnan gudunmuwa ga kasashen su domin taimakawa mutanen kasar su.
Idan wadannan hamshakan attajirai ba su tashi tsaye sun kawo dauki kamar yadda wasu suka fara yi a Chana da Italy da sauran kasashe ba, to mu na gudun idan zabe na gaba ya zo, babu sauran wanda zai yi musu kamfen, babu sauran wanda zai sayi simintin su. Kuma babu sauran wanda zai yi ajiyar kudade a bankunan su.
An yaba da kokarin da Shugaban Bankin FCMB, Peterside ya yi dangane da gidauniya da kuma Bankin Guaranty Trust Bank da ya Gina cibiyar kula da masu Coronavirus mai gadaje 100.
Wata babbar matsala ita ce, wakilan mu biyu sun kira lambobin 08009700010 da kuma 08000267662, wadanda aka ce a kira idan wani na tunanin ko ya kamu da cutar. Sun yi musu karyar cewa sun kamu, domin kawai mu gwada irin inganci da hobbasar da kasar nan ke yi.
Layi na farko kowane lokaci ba ya samuwa, ya na kan waya (busy). Na biyu da aka yi katarin samu kuma, babu wani gamsasshen bayani daga gare su.
Yayin da zuwa yanzu Afrika ta Kudu ta yi wa mutum sama da 15,000 gwaji, har yau a Najeriya wadanda aka yi wa gwaji ba su fi 200 kacal ba.
Matsawar babu hanyoyin gudanar da gwajin gaggawa, to mu na yaudarar kan mu ne kawai, amma ba a ma san yawan wadanda suka kamu ba.
Muddin gwamnati da hukuma ba ta nuna da gaske ta ke yi wajen daukar kwararan matakai ba, to jama’a ba za su dauki gargadin da ake yi musu da muhimmanci ba.
Yanzu a dauka a ce akwai mutum 2,550 masu matukar bukatar a yi musu gwaji, amma ba a yi ba, to Allah kadai ya san yawan wadanda za su kamu nan da kwanaki 30 masu zuwa.
Idan har abin ya kai gargara, tunda Gina cibiyoyin kula na da bukatar cin kudi masu yawa, me zai hana coci-coci da masallatai su sadaukar da filaye da maka-makan harabobin su domin a maida su cibiyoyin kulawa.
Za a iya amfani da filayen harabar coci-coci da masallatai ana yi wa jama’a gwaji. Gwamnati sai ta tashi tsaye, aikin gagarimi ne kwarai.
A gaggauta samar da sahihiyar hangar karbar gudummawa daga hamshakan attajirai, kuma a ci gaba da wayar wa jama’a kai.
Idan kunne ya ji, to jiki ya tsira!