Kwana uku kenan a jere Coronavirus na kashe mutum sama da 849 a duk rana a kasar Spain

0

Gwamnatin kasar Spain ta bada sanarwar mutuwar mutum 849 a rana daya.

Wannan adadin ya kawo yawan wadanda Coronavirus ta kashe a Spain sun kai mutum 8,189 a jimlace zuwa yau Talata.

Sannan kuma an samu wasu mutum 9,222 masu cutar a cikin kwana daya rak.

Yanzu kenan akwai mutum 94,417 masu cutar a Spain.

Idan aka hada da mutanen da suka muru a Spain, ya zama Coronavirus ta kashe mutum 38,000 a duniya, tun bayan barkewar cutar zuwa ranar Talata.

Gaba daya kididdigar lissafi ta nuna cewa kusan murum 800,000 ne cutar ta kama a fadin duniya.

Sannan kuma wata matsala da Spain ke kara fuskanta ita ce yadda jami’an lafiya da dama ke kamuwa da cutar.

A ranar Litinin Al Jazeera ta ruwaito cewa jami’an lafiya 12,298 ne suka kamu da cutar.

Wata jaridar Spain mai suna El Pais ta buga alkaluma cewa gaba dayan asibitoci da cibiyoyin kula da marasa lafiyar yankunan Spain 17 duk cike suke makil da masu dauke da cutar Coronavirus.

Jose Hernandez Mataimakin Farfesan Hakayyar Jama’a, ya ce wannan lamari ya yi muni kwarai kuma abin taoro ne matuka.

Hernandez kuma jami’in kula da lafiya ne mai rike da babban mukami a bangaren da ke Jami’ar Cordoba.

Amma kuma Daraktan Cututtukan Gaggawana Hukumar Lafiya ta Duniya, Mike Ryan ya ce akwai alamar an kusa gano maganin wannan cuta da ta addabi duniya baki daya.

Share.

game da Author