Coronavirus ta kashe Tsohon Shugaban Congo

0

Iyalan tsohon Shugaban Jamhuriyar Congo, Jacques Yhombi-Opango, sun bayyana mutuwar sa sakamakon kamuwa da cutar Coronavirus.

Sanarwar ta ce ya mutu a wani asibitin birnin Paris a kasar Faransa a ranar Litinin.

Ya mutu ya na da shekaru 81 a duniya. Iyalan sa sun ce dama ya na fama da wata rashin lafiya kuma sai ya sake kamuwa da cutar Coronavirus, wadda ita ce ajalin sa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa, AFP ne ya buga labarin mutuwar tsohon shugaban na Jamhuriyar Congo.

An haife shi a 1939, ya zama shugaban kasar Congo-Brazzaville 1977 zuwa 1979. Dennis SassouNgesso ne ya yi masa juyin mulki.

Daga baya ya yi kokarin shirya wa Ngessou juyin mulkin da bai nasara ba. An tsare shi daga 1987 zuwa 1990.

Ya kafa jam’iyya cikin 1992, ya shiga takara amma ya fadi zabe.

Coronavirus ta yadu zuwa kasashe 54 a nahiyar Afrika. Kasar Masar ce ta fi yawan wadanda suka mutu. Mutane 41 sun mutu a kasar zuwa yanzu. Sai kuma kasashen Aljeriya da Morocco da suka rasa mutane 35 da 33.

Kasar Afrika ta kudu ce ta fiyawan wadanda suka kamu da cutar. Zuwa yanzu suna da mutane akalla 1000. Najeriya na da mutane 135. mutum biyu sun mutu sannan uku sun warke daga cutar.

har yanzu masana na cewa akwai yiwuwar samun barkewar annuban da zai iya mamaye nahiyar Afrika din idan ba a kawo mata dauki ba ganin yadda mutanen yankin ke fama da talauci da karancin asibitoci irin na zamani.

Share.

game da Author