An samu karin mutum daya da ya kamu da coronavirus a jihar Bauchi, yanzu mutum 3

0

Mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Baba Tela ya bayyana cewa an samu karin mutum daya da ya kamu da cutar coronavirus jihar.

Baba Tela ya ce wannan mutum yana da shekaru 57 ne a duniya kuma tuni har an aika dashi asibitin koyarwa na Jami’ar tafawa Balewa domin a ci gaba da kulawa da shi.

Mataimakin gwamnan ya koka cewa har yanzu ba a dibi jini wadanda ake zaton sun yi cudanya da wadanda suka kamu da cutar ba a jihar duk da sun bibbi sun gano su.

An dibi jini akalla mutane 70 a jihar, amma 21 aka dawo da sakamamkon su.

A ranar talata Hukumar NCDC ta sanar cewa wasu mutum hudu sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya ranar Litinin.

Hukumar ta fadi haka ne ranar Talata da misalin karfe 11:15 na safe.

3 a jihar Osun, 1 a jihar Ogun. Sai kuma bayyanan wannan na jihar Bauchi da aka fadi da yammacin Talata.

A yanzu dai mutum 135 ne ke dauke da cutar, 8 sun warke, biyu sun mutu.

Legas – 81
FCT – 25
Ogun – 5
Enugu – 2
Ekiti – 1
Oyo – 8
Edo – 2
Bauchi – 2
Osun – 4
Ribas – 1
Benuwai – 1
Kaduna – 3

Za a iya samun Karin yawan mutanen da suka kamu da cutar a kasar nan ganin yadda gwamnati ta maida hankali wajen gano wadanda suka yi cudanya da wadanda suka kamu.

A jawabin da shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi wa ‘yan Najeriya ranar lahadi ya ce gwamnati ta saka dokar garkame garin Abuja da Legas na makonni biyu har sai an kammala yin gwajin wadanda ake zargin sun kamu da cutar.

Attajirai da manyan bankunan Najeriya suna ta aikawa da gudunmawarsu ga hukumar NCDC, domin tallafa mata wajen aikin kau da cutar da take yi.

Hatta ministocin Najeriya sun bada gudunmawar rabin albashin su na watan Maris ga wannan hukumar

Share.

game da Author