Kotu ta dakatar da Hukumar PCACC daga binciken Sarkin Kano Sanusi

0

Kotu a jihar Kano ta dakatar da hukumar binciken cin hanci da rashawa ta jihar PCACC daga bincken sarkin Kano Muhammadu Sanusi.

Hakan ya biyo bayan kara da sarki Sanusi ya shigar ya na kalubalantar wannan bincike da hukumar zata yi a kan sa.

Alkalin Kotun Lewis Allogoa ya ce kada wata hukuma ta kuskura ta binciki sarki Sanusi, yana mai cewa a bar komai yadda ya ke har sai an saurari karan da aka shigar a gabanta.

Dama can sarki Sanusi ya shigar da kara yana neman kotu ta dakatar da gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da shugaban hukumar PCACC Muhiyu Rimingado daga bincikar sa.

Dama kuma a baya kotu ta yi watsi da rahoton hukumar binciken da ta ce lallai a binciki sarki Sanusi sannan kuma ya sauka daga kujerar mulki, har sai an kammala bincike.

Alkali Lewis ya ce ba ayi wa Sarki Sanusi adalci ba domin ba a bashi daman kare kan sa ba a wannan bincike.

A baya dama, Kakakin PCACC ya bayyana wa manema labarai cewa an samu sarkin Kano Sanusi da hannu dumu-dumu a harkallar wasu filaye a unguwannin Hotoro, Arewa da Bubbugaje.

Cikin wadanda hukumar ke bincike har da Sarkin Shanun Kano, Shehu Dankadai, da makaman Kano Sarki Ibrahim.

Idan dai ba a manta ba, tun bayan nasarar da gwamnan Kano Abdullahi Ganduje yayi a zaben 2019, ake zaman doya da manja tsakanin sa da sarkin Kano Muhammadu Sanusi.

A dalilin haka, gwamna Ganduje ya kirkiro sabbin masarautu domin rage karfin mulkin sarkin Kano Sanusi.

Share.

game da Author