RIKICIN APC: ‘Yan sanda sun garkame hedikwatar APC a Abuja

0

Sufeto janar din ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya gargadi ‘ya’yan jam’iyyar APC daga kusantar hedikwatar jam’iyyar a Abuja ya na mai cewa har sai kotun daukaka kara ta yanke hukunci tukunna.

Hakan ya biyo bayan kukuncin da kotu a Abuja ta yanke na dakatar shugaban jam’iyyar Adams Oshiomhole daga shugabancin jam’iyyar.

sufeto Adamu ya ce da hukuncin kotun farko za su yi amfani da.

Yanzu dai ofishin uwar jam’iyyar zai ci gaba da zama a kulle har sai kotun daukaka kara ta yanke hukunci.

Idan ba a manta ba ranar Juma’a shugaban jam’iyyar APC Adam Oshiomhole ya bayyana wa manema labarai cewa bashi da Allan musurun da zai san ko Buhari na tare da shi ko A’a.

Oshiomhole ya ce shi dai ya tattauna da shugaban kasa Muhammadu Buhari amma hakan bai sa ya iya gane ko Buhari na tare da shi a wannan baraka da ta kunno kai a jam’iyyar APC ba wanda har tsige shi kotu ta yi.

” Ina so ku sani cewa wannan baraka da ta kunnu kai a jam’iyyat APC ba komai bace illa shirin siyasar 2023. Wasu na ganin muddun ina wannan kujera, tabbas ba za su samu yadda suke so ba shine kuka ga hakan na faruwa.

” Ni ina fadi musu cewa wasun su dake ta babatu, suna murza gashin baki ba za zu iya kawo koda kansila bane a jihohin su idan ba don jam’iyyar APC ba, sai dai ga su akan kujerun mulki suna ta tunkaho da fankama kaman su wasu abu ne a jihohin su ma a siyasance.

” Amma dai ni ba zan iya ce muku komai game da ganawa ta da shugaba Buhari ba. Domin ban san matsayin sa ba. Na dai na san mun tattauna sosai game da halin da jam’iyyar mu ke ciki.

Share.

game da Author