2023: Wasu ‘Yan siyasa ne ke shirya min tuggu don basu samun yadda suke so – Oshiomhole

0

Shugaban jam’iyyar APC Adam Oshiomhole ya bayyana wa manema labarai cewa bashi da Allan musurun da zai san ko Buhari na tare da shi ko A’a.

Oshiomhole ya ce shi dai ya tattauna da shugaban kasa Muhammadu Buhari amma hakan bai sa ya iya gane ko Buhari na tare da shi a wannan baraka da ta kunno kai a jam’iyyar APC ba wanda har tsige shi kotu ta yi.

” Ina so ku sani cewa wannan baraka da ta kunnu kai a jam’iyyat APC ba komai bace illa shirin siyasar 2023. Wasu na ganin muddun ina wannan kujera, tabbas ba za su samu yadda suke so ba shine kuka ga hakan na faruwa.

” Ni ina fadi musu cewa wasun su dake ta babatu, suna murza gashin baki ba za zu iya kawo koda kansila bane a jihohin su idan ba don jam’iyyar APC ba, sai dai ga su akan kujerun mulki suna ta tunkaho da fankama kaman su wasu abu ne a jihohin su ma a siyasance.

” Amma dai ni ba zan iya ce muku komai game da ganawa ta da shugaba Buhari ba. Domin ban san matsayin sa ba. Na dai na san mun tattauna sosai game da halin da jam’iyyar mu ke ciki.

Idan ba a manta ba kotu a makon da ta gabata ta yanke hukuncin dakatar da Oshiomhole daga shugabancin Jam’iyyar APC, sai dai bai kai ga daukaka kara ba ma wata kotun a Kano ta dawo da shi.

Share.

game da Author