CORONAVIRUS: Mutane sama da 10,000 sun mutu a Duniya, 700 sun kamu a Afrika

0

A rahoton ranar Juma’a da aka fitar zuwa yanzu mutanen da suka kamu da cutar coronavirus sun zarce 10,000 sannan wadanda suka kamu sun kai mutane 246,464, kuma mutane 10,049.

Akalla kasashe 182 suka kamu da cutar wadda ya nuna cewa kasashe 15 ne suka rage a duniya basu kamu da cutar.

Duk da cewa cutar ya na raguwa a kasar Chana, Kasashen Turai yanzu sun zarce Chana.

Haka kuma akalla mutane, 98,532 sun warke daga cutar.

TURAI

Kasar Italiya ce take kan gaba wajen yawan mutanen da suka kamu da cutar da mutane 41,035 sannan 3,405 sun mutu.

Kasar Italiya ce take kan gaba wajen yawan wadanda suka fi kamuwa da cutar a nahiyar Turai.

Sauran kasashen da acutar ta yi wa hawan kawara sun hada da Spain, Germany, France, Switzerland da the U.K.

Haka kuma kasar Amurka ma, mutane 14,366 sun kamu sannan mutane 217 sun rasu.

Shugaban kasar Amurka ya ce za a iya amfani da maganin zazzabi na Chloroquine wajen warkar da cutar.

A kasashen Afrika ma cutar tana ta dada yaduwa.

Zuwa ranar Alhamis mutane 700 ne suka kamu da cutar a kasashe 33 a Nahiyar. cases in about 33 countries.

A Najeriya, mutane 12 ne suka kamu da cutar, inda ana ci gaba da duba wasu da dama.

Jami’ar John Hopkins dake kasar Amurka ta bayyana cewa mutane sama da 200,000 ne ke dauke da cutar coronavirus a fadin duniya.

A dalilin haka kasashen duniya da dama sun hana jiragen sama sauka da tashi a kasashen su, sun rufe iyakokin kasashen su na kasa sannan wasu sun kafa dokar hana walwala domin dakile yaduwar cutar.

Bisa ga rahoton, mutane 201,000 ne suka kamu da cutar sannan 8,000 sun mutu.

Rahoton ya kuma bayyana cewa kasar Chana da a nan ne cutar ta fara barkewa ta fara samun ragowar yaduwar cutar.

Duk da haka kasar ce ta fi kowacce kasa a duniya yawan mutanen da suka kamu da cutar da yawan wadanda suka mutu.

Zuwa yanzu mutane 82 suka warke daga cutar sannan 3,000 sun mutu.

Italiya ce kasar dake biye da Chana inda a kasar mutane 31,500 suka kamu da cutar, 2,500 sun mutu.

Ma’aikatan kiwon lafiya sun yi kira ga kasashen duniya da su karfafa matakan hana yaduwar cutar amma kuma wasu kasashen duniya na kukan rashin isassun kayan gwajin cutar.

Idan ba a mata a ranar Laraba ne ba kungiyar kiwon lafiya (WHO) ta sanar cewa mutane 600 ne ke dauke da cutar sanna 41 sun warke a kasashen Afrika.

WHO ta kuma sanar ranar Alhamis cewa a cikin awa 24 mutane 17 sun mutu sannan mutane 633 na dauke da cutar a Nahiyar Afrika.

Kwayoyin cutar Corona Virus na daga cikin kwayoyin cutar dake sa a kamu da mura wanda idan yayi tsanani akan yi fama da matsalar cutar dake hana numfashi yadda ya kamata da ake kira (Middle East Respiratory Syndrome (MERS-CoV), da kuma cutar tsanannin mura da kan toshe makogoro.

Alamun kamuwa da cutar sun hada da matsala a kafofin wucewar iska a makogoro wato numfashi, yawan zazzabi, tsananin tari, da ciwo a makogoro.

Idan abin yayi tsanani, ya kan kai ga shakar iska ma ya gagara, sannan a samu matsalar sanyin hakarkari wato ‘Nimoniya’, kuma idan har ya yi tsanani matuka kodar mutum kan daina aiki kwata-kwata.

Za a iya kaucewa kamuwa da wannan cuta ta hanyar, yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu, sannan a rika rufe hanci da baki idan za ayi atishawa kuma a rika wankewa da dafa nama sosai ya nuna tubus kafin a ci da kwai.

A rika nisanta ko kuma zama kusa da wanda ya nuna alamun rashin lafiya musamman irin wadanda a ka lissafa a sama sannan a gaggauta zuwa asibiti da neman magani idan ba a da lafiya.

Share.

game da Author