CORONAVIRUS: Don Allah mu dauki wannan cuta da muhimmanci mutanen Arewa da Najeriya, Daga Fatima Lere

0

Har yanzu wasu musamman a yankin Arewan mu basu yadda cewa kwai cutar coronavirus ba. Sun maida abin ba’a da wasa. Za kaga mutane suna wasu irin Kalamai da bai dace ba ko kadan game da cutar.

Wasu na ganin Kawai karya ce ake yi wa mutane, wasu kuma na ganin babu ma cutar kwata-kwata.

Da yawa daga cikin mutane suna danganta abin da addini. Suna cewa an kirkiro cutarce domin a karya musulunci da dai sauransu.

Har wasu matasa sun yi mata waka suna murnar wai cutar ta shigo katsina a taya su murna. Wannan babban jahilci ne da rashin kan gado.

Cutar coronavirus ya somo asali ne daga kasar Chana, kuma in ba bayan a wannan mako ba, Kasarce ta fi kowacce kasa asarar mutane da wadanda suka kamu.

Sannan idan don a gama da musulunci ne, haryanzu babu wata kasar musulunci da ta zarce wata kasa da ba na musulmai ba yawan wadanda suka kamu ko kuma suka mutu.

Kasar Italiya da canne shugaban kiristocin Duniya, na Katolika yake, ta fi kowacce kasa yanzu yawan wadanda suka mutu.

A cikin kwana daya, akalla mutane 472 suka mutu nan take sannan mutane sama da 5000 sun kamu da cutar.

A Najeriya akwai mutane akalla 12 da aka tabbatar sun kamu sannan akwai dubbai da ake yi wa gwaji a wurare da dama.

Wannan cuta ba cuta ce da za a rika yi mata wani irin fassara ba, Cuta ce da ya kamata maida hankali matuka akai sannan a kiyaye daga kamuwa da ita.

Mutane su daina daukan ta da wasa.

Za ka ga hatta wadanda kake ganin ya kamata su sani, suna karyata yaduwar cutar suna cewa babu ita. Wasu daga cikin malamai suna karyata cutar, suna dangantata da addini. Bayan wannan musifa ce da duk duniya ke fama da ita.

Ya kamata Malamai maimakon su rika karyata wa su rika tunatar da mutane ne irin addu’o’in da ya kamata a rika yi domin Allah ya kawo mana sauki ba tunzura mutane da karerayi ba da kuma nuna wai ba haka bane, ko kuma ana so a karya musulunci ne.

A kiyaye da sharuddan bi don a kauce wa kamuwa da cutar.

Sannan kuma maimakon arika karyata cutar a nemi sani tukunna. Duk duniya kasashe na tattare mutanen su ne da wayar da su.

A kasar Saudiyya, hatta sallar juma’a an dakatar da yi a masallatan Makka da Madina da wasu manyan Masallatai dake kasar.

Sannan kuma matakan da gwamnatin Najeriya tayi na rufe makarantu yayi matukar Kyau. Mutane su maida Hankali matuka domin kiyaye wa.

Share.

game da Author